Karamar Sallah: An Jibge 'Yan Sanda 3200 a Imo Don Tabbatar da Tsaro

Karamar Sallah: An Jibge 'Yan Sanda 3200 a Imo Don Tabbatar da Tsaro

-Rundunar 'yan sanda ta jibge jami'anta sama da 3000 a jihar Imo don tabbatar da tsaro yayin bikin Sallah

- Rundunar ta 'yan sanda ta yi kira ga musulmai a jihar da su yi amfani da lokutan Sallah don yiwa kasa addu'o'i

- Hakazalika, hukumar tsaro ta NSCDC ta tura jami'anta don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo a ranar Talata ta ce ta tura jimillar jami’anta 3200 don tabbatar da isasshen tsaro a jihar yayin da musulmai muminai ke bikin karamar Sallah, Channels Tv ta ruwaito.

A wata sanarwa da aka ba manema labarai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Orlando Ikeokwu, rundunar ta tabbatar wa al'ummar Imo cewa tana hada kai da dukkan hukumomin tsaro a jihar.

Ikeokwu ya ce ‘yan sanda sun yi shiri yadda ya kamata don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a lokacin bikin.

KU KARANTA: Jerin Kasashen Da Basu Ga Wata Ba, Ba Kuma Za Su Yi Sallar Idi Gobe Laraba Ba

Karamar Sallah: An Jibge 'Yan Sanda 3200 a Imo Don Tabbatar da Tsaro
Karamar Sallah: An Jibge 'Yan Sanda 3200 a Imo Don Tabbatar da Tsaro Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yayin da yake taya musulmai murna a jihar, ya roke su da su yi amfani da lokacin domin yin addu'ar samun zaman lafiya da tsaro a jihar tare da hadin kai da zaman lafiyar kasa baki daya.

A halin yanzu, Kwamanda Janar na hukumar tsaro ta NSCDC, Ahmed Audi, ya ba da umarni ga Kwamandojin Shiyya na 15 na rundunar don karfafa tsaro a fadin jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ta NSCDC ta sabunta kokarin ta na tabbatar da tsaro kafin, yayin da kuma bayan bikin karamar Sallah.

NSCDC wacce ta bayyana hakan ta wata sanarwa da kakakinta, Olusola Odumosu, ta ce umarnin ya biyo bayan barazanar kai hare-hare daga bata gari a sassa daban-daban na kasar wanda dole ne a shawo kan matsalar domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: An Sanar Cewa Ba A Ga Watan Karamar Sallah Ba a Najeriya

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda ta Kwara ta gargadi 'yan siyasa a jihar kan amfani da filin Sallar Idi wajen tarukan siyasa, The Cable ta ruwaito.

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Mohammed Bagega, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Ajayi Okasanmi, kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya fitar a ranar Talata.

Ya ce wasu mutane na shirin hargitsa Sallar Idi don haka, ya gargadi mazauna yankin kan gudanar da tarukan siyasa a wurin da ake gudanar da Sallar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel