Sama da Kashi 75% Na Yan Najeriya Basa Jin Daɗin Gwamnatin Buhari, Sanatan APC

Sama da Kashi 75% Na Yan Najeriya Basa Jin Daɗin Gwamnatin Buhari, Sanatan APC

- Tsohon gwamnan jihar Imo kuma zaɓaɓɓen sanata a jam'iyyar APC yace sama da kashi 75% na yan Najeriya basa jin daɗin wannan gwamnatin

- Sanata Rochas Okorocha na jihar Imo yace ya kamata gwamnatin tarayya ta canza salon da take amfani dashi wajen yaƙi da matsalar tsaro

- Sanatan yace amafani da ƙarfin soji kaɗai ba zai warware matsalar tsaron da Najeriya ke fama dashi ba

Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha (APC, Imo) yace sama da kashi 75% na yan Najeriya suna takaicin abinda ke faruwa a ƙasar, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ba Za’a Ga Watan Sallah Ba Sai Ranar Laraba, Inji Hukumar NASRDA

Okorocha ya bayyana hakane a yayin da ya karbi baƙuncin dandazon mabiya addinin musulunci cikinsu harda masu nakasa domin shan ruwa tare ranar Litinin.

Sanatan yace ba yadda za'ai ayi tsammanin abu mai amfani daga wurin mutanen dake cikin takaici da bacin rai.

Sama da Kashi 75% Na Yan Najeriya Basa Jin Daɗin Gwamnatin Buhari, Sanatan APC
Sama da Kashi 75% Na Yan Najeriya Basa Jin Daɗin Gwamnatin Buhari, Sanatan APC Hoto: @RealRochas
Asali: Facebook

Okrocha yace:

"Ba zaka iya warware matsala ba sai ka gano tushenta, babban abinda ya jawo wa Najeriya matsalar tsaron da take fama dashi shine rashin adalci da talauci, sai kuma rashin ɗaukar mataki da gwamnati ke yi."

"Rashin adalci da kuma talauci da yayi wa yan ƙasa katutu shine babban abinda ya jawo mana matsalar tsaron da muke fama dashi."

KARANTA ANAN: Yan Bindiga na Buƙatar Tattaunawar Sulhu Da Malamai, Inji Tshohon Shugaban NHIS

"Idan gwamnati na son rage fushin da yan Najeriya ke ciki, to ya zama wajibe da magance rashin adalci tare da yin duk me yuwuwa domin saka al'ummarta cikin farin ciki."

Sanatan ya roƙi gwamnatin tarayya data canza salonta wajen yaƙi da matsalar tsaro, inda yace amfani da ƙarfin soji kaɗai bazai magance matsalar ba.

Ya kuma shawarci gwamnatin da ta fara tattaunawar neman zaman lafiya kuma ta saka mutane a ciki.

A wani labarin kuma Rundunar Soji Ta Bayyana Matakin da Zata Ɗauka Kan Zargin da Ake Mata a Jihar Zamfara

Rundunar Sojin ƙasar nan ta bayyana matakin da zata ɗauka kan zargin da ake yiwa wani jami'inta na kisan wani mai siyar da kankana a jihar Zamfara.

Kakakin rundunar, Muhammed Yerima, yace tuni suka fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano gaskiyar abinda ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262