'Yan Kasuwa Sun Tafka Asara Bayan Mummunar Gobara da Ta Yi Kaca-kaca da Kasuwa
- 'Yan kasuwa sun koka bisa asarar da suka tafka gabanin cinikin sallah mai zuwa nan gaba
- An ruwaito cewa, gobara ta yi kaca-kaca da kayayyakin 'yan kasuwa a wata kasuwa a Osogbo
- Hukumar kashe gobara ta kawo dauki inda aka yi nasarar kashe wutar bayan yin barna da yawa
‘Yan kasuwa a Kasuwar Igbona da ke Osogbo, Jihar Osun, a ranar Litinin sun koka bisa asarar da suka tafka bayan wata mummunar gobara da ta yi kaca-kaca da kayayyaki a shaguna da dama.
‘Yan kasuwan sun ce kayayyaki na miliyoyin nairori sun lalace a shagunansu kuma lamarin gobarar ya kassara kasuwancinsu, Daily Trust ta ruwaito.
Wasu mazauna garin sun ce gobarar ta tashi ne sakamakon tartsatsin wutar lantarki amma babu wani bayani a hukumance daga kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan (IBEDC) don tabbatar da hakan.
KU KARANTA: Ban da Alaka da 'Yan Ta'adda, Janar Abdulsalami Ya Yi Martani Kan Alakanta Shi da Ta'addanci
Daya daga cikin masu shagunan da wutar ta lalata kayansu, Mista Nicholas Balogun, ya ce an kira shi cewa shagon nasa na ci da wuta kuma a lokacin da ya isa wurin, babu abin da zai cire saboda wutar ta lakume shagon nasa gaba daya .
Wata 'yar kasuwa a kasuwar, Misis Sola Ebunolu, ta ce ta sayi sabbin kayayyaki ne da ta ke so ta sayar a lokacin Sallah amma gobarar ta lalata dukkan kayayyakin da ke cikin shagon na ta.
Jami'ar hulda da jama'a ta hukumar kashe gobara ta tarayya a jihar, Misis Adijat Basir, ta ce wutar za ta yi barna mai yawa idan da ba a hanzarta kashe ta ba.
KU KARANTA: Saboda Ayaba, Wani Soja Ya Bindige Dan Kasuwa a Jihar Zamfara
A wani labarin, Gobara ta lakume wani bangare na kasuwar Cairo a karamar hukumar Oshodi-Isolo da ke jihar Legas.
Jaridar TheCable ta rahoto cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 8 na daren ranar Alhamis, kuma ta shafi bangaren kaya na kasuwar.
Ba a san abin da ya haddasa wutar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Rahotanni sun ce kayyaki na miliyoyin nairori sun kone saboda da yawa daga cikin shagunan gobarar ta shafa.
Asali: Legit.ng