Shugaban hafsun soji ya bukaci jami'ai su yi adalci wajen daukar sabbin sojoji

Shugaban hafsun soji ya bukaci jami'ai su yi adalci wajen daukar sabbin sojoji

  • Shugaban hafsun soji ya ziyarci sansanin tantance daukar ma'aikata a dajin Falgore da ke Kano
  • Ya bukaci jami'an da ke aikin tantance daukar sabbin sojojin da su kasance masu gaskiya da adalci
  • Ya kuma ba da tabbacin cewa, zai samar da abubuwan da ake bukata domin gudanar da aikin cikin sauki

Faruk Yahaya, shugaban hafsan sojojin Najeriya, ya yi kira ga hafsoshi da ma’aikatan da ke gudanar da aikin tantance zababbun ma’aikatan rukuni na 81 na shiga aikin sojojin Najeriya da su kasance masu adalci da gaskiya.

Yahaya ya ba da umarnin ne a ranar Asabar, lokacin da ya ziyarci cibiyar horar da sojojin Najeriya da ke sansanin Falgore a jihar Kano, inda ake gudanar da aikin tantancewar.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar Onyema Nwachukwu ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 7 ga watan Agusta a Abuja, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ku kai yakin har zuwa mafakar makiya, COAS, Janar Yahaya ya umarci sojoji

Shugaban hafsun soji ya ziyarci sansanin daukar sabbin sojoji na Falgore a Kano
Shugaban hafsun sojoji da wasu jami'an soji | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Babban hafsan sojojin ya bukaci jami’an da su gudanar da ayyukansu cikin himma da kwarewa, ya kara da cewa dole ne ma’aikata su kasance masu adalci da tsayuwa wajen gudanar da aikin.

COAS ya ba da tabbacin samar da abubuwan da ake bukata ga sojoji

Ya kuma ba su tabbacin goyon bayan hedkwatar sojoji wajen ba su kayan aiki da sauran abubuwan more rayuwa da ake bukata don samun nasarar gudanar da aikin tantance wadanda ya kamata a dauka.

Yahaya ya yabawa gwamnatin jihar Kano saboda tallafawa sojojin Najeriya wajen inganta kayayyakin more rayuwa a cibiyar da ke a Falgore.

Ya karfafawa tare da yabawa masu neman aikin bisa jajircewarsu da kishinsu na yin aikin sojan Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar ya bayyana a cikin sanarwar cewa daukar aikin wani bangare ne na kokarin da sojojin Najeriya ke yi na kara karfin ma'aikata.

Meye yasa ake atisayen daukar aikin soji a sansanin Falgore?

Kara karanta wannan

Ta'addanci: IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta

Ya ce ana gudanar da atisayen ne a Falgore don bai wa wadanda za a dauka aiki damar zama a wurare domin su gane hakikanin yanayin kasa da yanayin da za su fuskanta yayin horo da lokacin gudanar da aikin soja.

A cewarsa, wannan dabarar tana ba da tabbaci ga ginshikan falsafar COAS, wanda ya danganta da kwarewa, kyakkyawan shiri, gudanarwa da hadin gwiwa, kamar yadda The Eagle Online ta tattaro.

Ya ce ziyarar ta kasance wani babban abin karfafa gwiwa ga masu son shiga aikin na soji.

Ku kai yakin har zuwa mafakar makiya, COAS, Janar Yahaya ya umarci sojoji

A wani labarin, Babban hafsan Sojojin kasa (COAS), Faruk Yahaya, ya umarci sojojin Najeriya da su kai yaƙi zuwa maboyar 'yan ta'adda da' yan fashi.

Kwamandan rundunar ya bayar da umarnin a ranar Juma’a, 7 ga watan Agusta, lokacin da yake yi wa sojoji jawabi a sansanin Fort Muhammadu Buhari dake Daura, jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani tsakanin kudin intanet na Najeriya da Bitcoin

Yahaya ya bayyana cewa duk da cewar akwai ƙalubale, amma yakamata sojoji su ƙuduri aniyar cin nasarar yaƙin, The Sun ta ruwaito.

Yace:

"Wannan shine abin da muke yi kuma wannan shine abin da za mu ci gaba da yi. Domin duk wurin da na wuce, sakona kenan.
Dole ne mu kai yaƙin zuwa wuraren abokan gaba a nan arewa maso yamma har ma a arewa maso gabas inda muke gudanar da su.''

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: