Rundunar 'yan sanda ta cafke mutum 8 da ake zargin Masu Garkuwa da Mutane Ne

Rundunar 'yan sanda ta cafke mutum 8 da ake zargin Masu Garkuwa da Mutane Ne

- Rundunar 'yan sanda a jihar Osun ta yi nasarar kame wasu gungun masu satar mutane

- Rundunar ta bayyana cewa, ta bi diddigin mutanen ne, inda ta gano sun gudo ne daga Benue

- Rundunar ta kuma yi kira ga al'ummar jihar ta ba da hadin kai da goyon baya ga 'yan sanda

Rundunar ‘yan sanda a Osun ta ce ta cafke mutum takwas da ake zargin tawagar masu satar mutane ne da suka koma jihar don buya bayan aikata barna a jihar Benue, Vanguard ta ruwaito.

SP Yemisi Opalola, mai magana da yawun rundunar, ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa an kama wadanda ake zargin ne a ranar Juma’a a kauyen Omo Ijesa, bayan rahotannin sirri da rundunar ta samu.

Opalola ya ci gaba da cewa, lokacin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa cewa sun kashe wacce suka kashe ta karshe, Misis Akiishi Catherine, mai shekaru 65, da kuma wasu mutum uku a barnar da suka yi a baya.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Saki Dalibai 27 Na Kwalejin Noma Dake Kaduna

Rundunar 'yan sanda ta cafke mutum 8 da ake zargin 'yan bindiga ne
Rundunar 'yan sanda ta cafke mutum 8 da ake zargin 'yan bindiga ne Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

“An kama wadanda ake zargin ne a ranar 7 ga watan Mayu, biyo bayan sahihan bayanan sirri da rundunar ta samu kuma ta yi aiki a kan bin diddigin lamarin satar wata mata mai shekaru 65, Misis Akiishi Catherine a jihar Benue.

“Kwamishinan 'yan sanda a Osun, Olawale Olokode ne ya jagoranci aikin.

“Kafin kamun, binciken 'yan sanda ya nuna cewa wadanda ake zargin sun koma Osun bayan sace matar a matsayin wata dabara ta gujewa kamun ‘yan sanda a Benue.

Kakakin ya ce "wadanda ake zargin sun kuma yi shirin amfani da Osun a matsayin mafaka don tattaunawa da karbar kudin fansa duk da cewa sun kashe matar cikin ruwan sanyi."

Ya ce wadanda ake zargin da shekarunsu ba su wuce 18 zuwa 25 ba, sun yi ikirarin kashe wacce suka kashe ta karshe da kuma wasu mutum uku.

“Za a mika wadanda ake zargin ga rundunar 'yan sanda ta Benue da zaran an kammala bincike na farko ’’, in ji shi.

Ya ce kwamishinan 'yan sanda, Olokode, ya yaba wa jami'an 'yan sanda bisa nasarar aikin.

Olokode ya tabbatarwa da ‘yan jihar cewa babu wani mafaka na masu aikata laifi a jihar.

Ya lura cewa sabbin tsarukan 'yan sanda na Sufeto Janar na 'yan sanda, Usman Baba, ya taimakawa rundunar wajen sake fasalin dabarun ta na magance laifuka a jihar.

Kwamishinan ya yi kira ga ’yan jihar da su ba da goyon baya da hadin kai ga 'yan sanda don wanke jihar daga masu aikata laifuka da ke barazana ga zaman lafiya, tsaro da amincin mutane.

KU KARANTA: An Sako Shugaban Miyetti Allah da Aka Sace, Ya Ce Ba 'Yan Bindiga Ne Suka Sace Shi Ba

A wani labarin, Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kubutar da mutum 13 daga hannun 'yan bindiga da suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar ta fitar a daren jiya Laraba ba ta bayyana lokacin da lamarin ya faru ba.

Mutanen a cewar Kwamishinan Tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, sun je Bakin Kasuwa da ke Karamar Hukumar Chikun domin yin aikatau a wata gona lokacin da 'yan bindigan suka kai musu harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel