Rashin bayyanar Alkali ya hana cigaban shari’ar patience Jonathan na $15.5m da aka rufe a asusun ajiyarta
- Rashin bayyanar Justis Mohammed Idris na kotun tarayya dake jihar Legas, a ranar Talata, ya hana cigaban shari’ar matar tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan, Patience
- Alkalin kotun bai samu halartar shari’ar ba sakamakon tafiya da yayi zuwa wurin wani taro nasu na alkalai
- Patience ta shigar da kara a 2016, inda ta kalubalanci hukumar yaki da rashawa akan hana ta cire kudi daga asusun ajiyarta na bankin Skye, wanda ke dauke da kudi da zasu kai kimanin $15.5m
Rashin bayyanar Justis Mohammed Idris na kotun tarayya dake jihar Legas, a ranar Talata, ya hana cigaban shari’ar matar tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan, Patience, inda hukumar yaki da rashawa ta daskarar mata da asusun ajiyarta.
Alkalin kotun bai samu halartar shari’ar ba sakamakon tafiya da yayi zuwa wurin wani taro nasu na alkalai, sakamakon haka an mayar da shari’ar zuwa 19 ga watan Yuni.
Patience ta shigar da kara a 2016, inda ta kalubalanci hukumar yaki da rashawa akan hana ta cire kudi daga asusun ajiyarta na bankin Skye, wanda ke dauke da kudi da zasu kai kimanin $15.5m.
A zaman farko masu bayar da shaida sun fara gabatar da shaidunsu game da shari’ar, saboda haka a zama nag aba Idris yace cigaba ne kawai za’ayi da sauraren karar, kamar yanda NAN ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Mahaifin budurwar da saurayinta ya kashe ya fadawa saurin nata cewa sai ya auri gawar diyar tasa
A baya Legit.ng ta ruwaito cewa brahim Shekarau da Aminu Wali da kuma Mansur Ahmed zasu bayyana a ofishin na EFCC ne akan kudaden da ake zargin sun kasa N950m, a gidan Ibrahim Shekarau gabanin zuwan zaben shekarar 2015 a tsakanin ‘yan jam’iyyarsu ta PDP.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng