Kwanaki kadan bayan sace ta, an sako dalibar jami'ar jiha ta Abia da aka sace

Kwanaki kadan bayan sace ta, an sako dalibar jami'ar jiha ta Abia da aka sace

- Dalibar da aka sace 'yar jami'ar jiha ta Abia ta samu 'yanci daga hannun masu garkuwa da mutane

- Gwamnatin jihar ta bayyana jin dadinta da sakin dalibar, ta kuma bayyana cewa za ta dauki mataki

- Hakazalika ta yabawa wadanda suka taimaka wajen tabbatar da an kubutar da dalibar da hannun 'yan ta'adda

Dalibar da aka sace na Jami'ar Jihar Abia da ke Uturu, (ABSU), ta samu 'yanci daga hannun masu garkuwa da mutane.

Gwamna Okezie Ikpeazu ya sanar da haka a karshen mako, inda ya godewa jami'an tsaro da kuma sashen gudanarwar ABSU kan aikin da aka yi mai kyau.

Ya kara da cewa za a dauki mataki kan wadanda suka yi satan saboda jihar Abia ba zata iya juran zama da masu aikata laifi ba.

An tattaro cewa a ranar Laraba, 5 ga Mayu, 2021, masu garkuwa da mutane sun tsare wata mota Sienna da ke dauke da fasinjoji, ciki har da daliban ABSU, a Okigwe da ke Jihar Imo.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Saki Dalibai 27 Na Kwalejin Noma Dake Kaduna

Kwanaki kadan bayan sace ta, an sako dalibar jami'ar jiha ta Abia da aka sace
Kwanaki kadan bayan sace ta, an sako dalibar jami'ar jiha ta Abia da aka sace Hoto: lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Daily Trust ta kuma tattaro daga majiyoyin gwamnati cewa daliban ABSU uku ne lamarin ya rutsa da su sannan biyu suka tsere yayin da wadanda suka sace su ke shiga daji.

Lamarin ya kai ga jami'an tsaro na jihohin Abia da Imo sun hada karfi da karfe don ceto dalibar da duk wadanda ke hannun masu garkuwar.

Kwana uku bayan namijin kokarin, sakamako mai kyau ya fito tare da Gwamnan Abia dake nuna farin cikinsa tare da tabbatar wa mutanen jihar cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar kare rayuka da dukiyoyi.

“Ina cikin matukar farin ciki da annashuwa na sanar da cewa an saki dalibar ABSU guda daya da aka sace wacce ke hannun wadanda suka sace wasu mutane kwanakin baya a kan hanyar Okigwe-Uturu.

“Na yi magana da ita da mahaifiyarta mintocin da suka gabata kuma ina son in gode wa Allah, jami’anmu na tsaro da sashen gudanarwar ABSU kan aikin da aka yi wanda ya kai ga wannan kyakkyawan labari.

“Gwamnatinmu tun daga wannan lokacin ta dauki matakan karfafa tsaro a yankin da lamarin ya faru don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi wanda shi ne aiki na na daya a matsayin Gwamna kuma aiki ne tilo da ba zan taba yin wasa da shi ba.

"Lallai za mu dauki mataki kan wadanda suka sace dalibar mu saboda ba za mu zauna tare a wannan jihar da masu laifi ba," in ji Ikpeazu.

KU KARANTA: Rundunar 'yan sanda ta cafke mutum 8 da ake zargin Masu Garkuwa da Mutane Ne

A wani labarin, Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kubutar da mutum 13 daga hannun 'yan bindiga da suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar ta fitar a daren jiya Laraba ba ta bayyana lokacin da lamarin ya faru ba.

Mutanen a cewar Kwamishinan Tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, sun je Bakin Kasuwa da ke Karamar Hukumar Chikun domin yin aikatau a wata gona lokacin da 'yan bindigan suka kai musu harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.