Karya Ne El-Rufai Bai Taba Cewa Buhari Bai Cancanci Shugabancin Najeriya Ba – Gwamnatin Kaduna

Karya Ne El-Rufai Bai Taba Cewa Buhari Bai Cancanci Shugabancin Najeriya Ba – Gwamnatin Kaduna

- Gwamnatin jihar Kaduna ta karyata wani wallafar jaridar yanar gizo da aka alakanta da gwamnanta kan Shugaba Muhammadu Buhari

- Gwamnatin ta Kaduna ta ce El-rufai bai taba cewa Buhari bai da karfin tunani da lafiyar jagorantar Najeriya ba

- Ta bayyana hakan a matsayin makircin wasu mutane don haifar da rudani a siyasar kasar

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce Nasir El-Rufai, gwamnanta, bai bayyana Buhari a matsayin wanda ba shi da karfin tunani da lafiyar iya jagorantar Najeriya ba.

Wannan magana an danganta ta ne ga gwamnan a wani rahoto da wani dandalin yanar gizo ya wallafa.

KU KARANTA KUMA: An Kashe Jami’in Dan Sanda, An Kama Yan Shi’a 49 Bayan Sabon Zanga-zanga Da Aka Yi A Abuja

Karya Ne El-Rufai Bai Taba Cewa Buhari Bai Cancanci Shugabancin Najeriya Ba – Gwamnatin Kaduna
Karya Ne El-Rufai Bai Taba Cewa Buhari Bai Cancanci Shugabancin Najeriya Ba – Gwamnatin Kaduna Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

A wata sanarwa a ranar Asabar, Samuel Aruwan, kwamishanan tsaron cikin gida na Kaduna, ya ce ikirarin karya ne.

Ya ce wadanda ke da alhakin wallafar suna neman haifar da "tashin hankali da rudani me a cikin siyasar kasar", jaridar The Cable ta ruwaito.

Aruwan ya bukaci jama'a da su yi watsi da dandalin da ke "kokarin wucewa a matsayin shahararriyar jaridar yanar gizo don yada makircinsu".

Sanarwar ta ce: "An wallafa wani rahoton bogi a yanar gizo a kan Shugaba Muhammad Buhari inda suka danganta shi ga Gwamna Nasir El-Rufai.

“Manufar tawagar da ke da alhakin yada labarin karyar da makircin shine, saboda haifar da rikici da rudani a cikin siyasar kasar.

“Dukkanin labaran an kirkiresu ne, kuma suna kokarin wucewa a matsayin shahararriyar jaridar yanar gizo don yada makircinsu.

"Gwamnatin Jihar Kaduna ta bukaci jama'a da su yi watsi da wannan wallafar kuma su dauke shi a matsayin karya ce kawai."

KU KARANTA KUMA: Peter Aliyu: Sadu da Mai Aikin Share Titi Wanda Ya Daukaka Ya Zama Babban Hadimin Wani Gwamnan Najeriya

A wani labarin, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana takwaransa na Kaduna a matsayin daya daga cikin makiyan Najeriya.

Gwamna Ortom ya yi wannan ikirarin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Terver Akase ya aika wa Legit.ng a ranar Asabar, 8 ga watan Mayu.

Gwamnan na Benuwai yana mayar da martani ne ga wata sanarwa da aka alakanta da El-Rufai wanda ya zargi Ortom da amfani da rashin tsaro a jiharsa wajen kai hari ga gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel