An Kashe Jami’in Dan Sanda, An Kama Yan Shi’a 49 Bayan Sabon Zanga-zanga Da Aka Yi A Abuja

An Kashe Jami’in Dan Sanda, An Kama Yan Shi’a 49 Bayan Sabon Zanga-zanga Da Aka Yi A Abuja

- Rundunar yan sanda ta sanar da rasa wani jami'inta sakamakon wata zanga-zangar yan shi'a a Abuja

- Lamarin ya afku ne a ranar 7 ga watan Mayu wanda yayi daidai da tattakin da suke yi a ran Juma'ar karshe ta Ramadan

- An kuma yi nasarar cafke 'ya'yan kungiyar guda 49, sannan za a gurfanar da su da zaran an kammala bincike

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da kisan wani jami’inta, ASP Adama Ezekiel, yayin wata zanga-zangar da ‘yan kungiyar shi’a (IMN) suka yi.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar FCT, Mariam Yusuf, mataimakiyar Sufeta ta ’yan sanda, ce ta sanar da mutuwar Ezekiel a cikin wata sanarwa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ta ce 'yan sanda sun yi nasarar dawo da kwanciyar hankali a Berger Roundabout bayan “ta tarwatsa wata mummunar zanga-zangar ta haramtacciyar kungiyar IMN cikin kwarewa” a ranar Juma'a.

An Kashe Jami’in Dan Sanda, An Kama Yan Shi’a 49 Bayan Sabon Zanga-zanga Da Aka Yi A Abuja
An Kashe Jami’in Dan Sanda, An Kama Yan Shi’a 49 Bayan Sabon Zanga-zanga Da Aka Yi A Abuja Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Ortom Ya Yiwa El-Rufai Wankin Babban Bargo, Ya Ce Yana Daya Daga Cikin Makiyan Najeriya Na Hakika

"Abin takaici, mambobin kungiyar da aka wargaza sun ci gaba da kai hare-hare, suna lalata dukiyoyin jama'a da kuma kai hari ga 'yan kasa da basu ji ba basu gani ba ciki har da jami'an' yan sanda ta hanyar amfani da muggan makamai kamar su adda, adduna da wuka, da sauransu," in ji Yusuf a cikin sanarwar.

“Abun bakin ciki, daya daga cikin Jami’an 'Yan Sanda, ASP Adama Ezekiel, da aka tura domin dawo da kwanciyar hankali yayin zanga-zangar ta tashin hankali, ya biya babban sakamako saboda mummunan harin da aka kai masa inda wani daga cikin fusatattun masu zanga-zangar ya daba masa wuka. An kama mambobin kungiyar guda 49 kuma za a gurfanar da su a kotu bayan an kammala bincike.

“Dangane da abin da ke sama, Kwamishinan ‘yan sanda CP. Bala Ciroma na mika sakon ta'aziya ga iyalan jami'in da ya mutu wanda ya yi babban aiki wajen yi wa kasa hidima.”

Sanarwar ta yi gargadin cewa rundunar ba za ta lamunci ci gaba da kai hare-hare kan ma'aikatanta, kayan aikinta ko wasu kadarorin jama'a da mambobin "haramtattun kungiyar" ke yi ba tare da yin kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu tare da bin doka.

Shaidun gani da ido sun ce ‘yan sanda sun cafke mambobin ne a cikin motocin bas dinsu yayin da ake jin karar harbe-harbe a kewayen hanyar Berger da ke Abuja.

An ce jerin gwanon ya yi daidai ne da tattakin da mutanen Falasdinu ke gudanarwa a duk ranar Juma’ar karshe ta Ramadan.

KU KARANTA KUMA: An Bankado Manyan Mutanen Dake Daukar Nauyin Ta’addanci a Najeriya – Malami

A wani labarin, da yawa daga cikin masu amfani da kafafen sadarwa sun caccaki gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai bayan ya bukaci a tarwatsa yan bindigar da suka yi garkuwa da dalibai 29 na Kwalejin Gandun Daji, Afaka, ko da kuwa haka zai janyo wasu dalibansu rasa ransu.

El-Rufai a wata tattaunawar yanar gizo da shugabannin Africa suka shirya karkashin Pastor Ituah Ighodalo, ranar Alhamis, ya ce gwamnatin jihar a shirye take ta hakura da rayuwar daliban a kokarin murkushe yan bindigar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel