Ortom Ya Yiwa El-Rufai Wankin Babban Bargo, Ya Ce Yana Daya Daga Cikin Makiyan Najeriya Na Hakika

Ortom Ya Yiwa El-Rufai Wankin Babban Bargo, Ya Ce Yana Daya Daga Cikin Makiyan Najeriya Na Hakika

- Gwamna Samuel Ortom ya bayyana takwaransa na jihar Kaduna a matsayin makiyin Najeriya

- Gwamnan na Benuwai ya kuma bayyana cewa Malam Nasir El-Rufai na daya daga cikin wadanda ke yaudarar Shugaba Buhari

- Gwamnan ya kuma bayyana abokin aikin nasa a matsayin gwarzon kabilanci kuma mai kishin addini

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana takwaransa na Kaduna a matsayin daya daga cikin makiyan Najeriya.

Gwamna Ortom ya yi wannan ikirarin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Terver Akase ya aika wa Legit.ng a ranar Asabar, 8 ga watan Mayu.

Gwamnan na Benuwai yana mayar da martani ne ga wata sanarwa da aka alakanta da El-Rufai wanda ya zargi Ortom da amfani da rashin tsaro a jiharsa wajen kai hari ga gwamnatin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Peter Aliyu: Sadu da Mai Aikin Share Titi Wanda Ya Daukaka Ya Zama Babban Hadimin Wani Gwamnan Najeriya

Ortom Ya Yiwa El-Rufai Wankin Babban Bargo, Ya Ce Yana Daya Daga Cikin Makiyan Najeriya Na Hakika
Ortom Ya Yiwa El-Rufai Wankin Babban Bargo, Ya Ce Yana Daya Daga Cikin Makiyan Najeriya Na Hakika Hoto: @GovSamuelOrtom
Asali: Twitter

Gwamnan na Kaduna ya ci gaba da cewa, Ortom yana amfani da dabaru ne domin rufe abin da ya kira gazawar gwamnan jihar Benuwai.

Sanarwar ta bayyana cewa harin da El-Rufai ya kaiwa Gwamna Ortom don kawai yayi farin jini ne a gaban fadar shugaban kasa.

Gwamna Ortom ya kara zargin El-Rufai da inganta rashin tsaro a kasar ta hanyar kalaman sa.

KU KARANTA KUMA: An Bankado Manyan Mutanen Dake Daukar Nauyin Ta’addanci a Najeriya – Malami

Wani bangare na jawabin ya ce:

“Nasir el-Rufai mashahuri ne, gwarzon kabilanci, kuma mai tsananin son addini wanda yake kin duk wanda ba addinin shi daya da shi ba. Yana cikin yan tsirarun mutanen da suka batar da Shugaba Muhammadu Buhari.

"El-Rufai na daya daga cikin makiyan kasar nan na hakika wadanda ba sa boye bambancin ra'ayinsu ta hanyar fifita son zuciya da kabilanci sama da kyawawan dabi'u da suka hada Najeriya a tsawon shekarun da suka gabata."

A wani labarin, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shawarci yankin kudu maso gabas da su nemi takarar shugaban kasa ta hanyar siyasa, maimakon yin barazanar.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, El-Rufai ya bayar da wannan shawarar ne a ranar Laraba, 6 ga watan Mayu, a wani taro ta shafin yanar gizo da kungiyar Shugabancin Afirka ta shirya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng