Peter Aliyu: Sadu da Mai Aikin Share Titi Wanda Ya Daukaka Ya Zama Babban Hadimin Wani Gwamnan Najeriya

Peter Aliyu: Sadu da Mai Aikin Share Titi Wanda Ya Daukaka Ya Zama Babban Hadimin Wani Gwamnan Najeriya

- Gwamna Bello na jihar Kogi ya nada Peter Aliyu, mai aikin share-share, a matsayin babban mai taimaka masa kan tsafta

- A cewar SSG na jihar, an nada Aliyu ne saboda kwazo da jajircewarsa

- Har zuwa lokacin da aka nada shi, Aliyu ya kasance mai shara a karkashin shirin tsafta na Geemoney a jihar Kogi

Daga aikin share-share a karkashin shirin hadin gwiwa na gwamnatin jihar Kogi, Geemoney Cleaning Scheme, Peter Aliyu ya daukaka ya zama Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Yahaya Bello kan Tsafta.

An sanar da nadin Aliyu ne a wata sanarwa da Sakatariyar Gwamnatin Jihar (SSG), Dakta Folashade Arike Ayoade, ta sa wa hannu, aka kuma aika wa Legit.ng a ranar Asabar, 8 ga Mayu.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Gumi Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Idan 'Yan Bindiga Suka Sace Dansa

Peter Aliyu: Sadu da Mai Aikin Share Titi Wanda Ya Daukaka Ya Zama Babban Hadimin Wani Gwamnan Najeriya
Peter Aliyu: Sadu da Mai Aikin Share Titi Wanda Ya Daukaka Ya Zama Babban Hadimin Wani Gwamnan Najeriya Hoto: @PlusTVAfrica
Asali: Twitter

An sanar da nadin Aliyu wanda ke da matsalar magana a majalisar zartarwar jihar tare da sauran sabbin wadanda gwamnatin ta bai mukamai a cikin gwamnatin jihar.

Me yasa aka nada Aliyu

Da yake bayyana dalilin nadin na Aliyu, SSG din ya ce Gwamna Bello ya gamsu da yadda matashin ya kasance mai kwazo, himma da jajircewa bayan lura da shi na wani lokaci.

Sakatariyar ta lura cewa halayen da Gwamna Bello ya lura su sun kuma sa Aliyu yana burge mutane da yawa wadanda suka yaba da nadin nasa.

KU KARANTA KUMA: An Bankado Manyan Mutanen Dake Daukar Nauyin Ta’addanci a Najeriya – Malami

Dokta Ayoade ta kara da cewa Gwamna Bello bai dauki nakasar Aliyu na rashin iya magana, "a matsayin cikas gareshi ba illa ya dauki hakan a matsayin wata hanya ta shigar da shi da kuma tabbatar wa duniya cewa gaskiya ne batun cewa a nakasa ma akwai iyawa."

A wani labarin, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shawarci yankin kudu maso gabas da su nemi takarar shugaban kasa ta hanyar siyasa, maimakon yin barazanar.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, El-Rufai ya bayar da wannan shawarar ne a ranar Laraba, 6 ga watan Mayu, a wani taro ta shafin yanar gizo da kungiyar Shugabancin Afirka ta shirya.

Gwamnan ya bayyana cewa siyasa tana da alaƙa da tattaunawa da shawo kan wasu don su zaɓe ku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng