Yanzu-Yanzu: Hotunan Ɗaliban Afaka Yayin Da Aka Sada Su Da Iyalansu

Yanzu-Yanzu: Hotunan Ɗaliban Afaka Yayin Da Aka Sada Su Da Iyalansu

- Daga karshe, gwamnatin jihar Kaduna ta mika daliban Kwallejin Afaka ga iyayensu

- Hakan ya biyo bayan ceto daliban sannan aka kai su asibiti don likitoci su duba su

- Iyayen daliban sun yi kira ga gwamnati ta zage damtse don samar da tsaro a makarantun

Daga ƙarshe, ɗaliban kwalejin tarayya na nazarin gandun daji da ke Afaka a jihar Kaduna sun sadu da Iyalansu, The Cable ta ruwaito.

Yan bindiga sun sace ɗaliban ne a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2021.

Duk da cewa su 39 aka sace yayin harin, an sako 10 daga cikinsu tunda farko.

Yanzu-Yanzu: Ɗaliban Afaka da Aka Sace Sun Sadu da Iyalansu
Yanzu-Yanzu: Ɗaliban Afaka da Aka Sace Sun Sadu da Iyalansu. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Yanzu-Yanzu: Ɗaliban Afaka da Aka Sace Sun Sadu da Iyalansu
Yanzu-Yanzu: Ɗaliban Afaka da Aka Sace Sun Sadu da Iyalansu. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mutanen Gari Sun Ƙona Ƴan Bindiga Uku Ciki Har da Mace a Sokoto

Yanzu-Yanzu: Ɗaliban Afaka da Aka Sace Sun Sadu da Iyalansu
Yanzu-Yanzu: Ɗaliban Afaka da Aka Sace Sun Sadu da Iyalansu. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Amma sauran daliban ba a sako su ba har sai ranar Laraba - bayan tsare su na makonni bakwai.

Yanzu-Yanzu: Ɗaliban Afaka da Aka Sace Sun Sadu da Iyalansu
Yanzu-Yanzu: Ɗaliban Afaka da Aka Sace Sun Sadu da Iyalansu. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Gwamnatin jihar Kaduna ta garzaya da ɗaliban zuwa asibiti ne domin a duba lafiyarsu kafin daga bisani a yau Juma'a aka sada su da iyalansu.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Jarida, Sunyi Garkuwa da Matafiya da Dama a Katsina

Da suka jawabi kan afkuwar lamarin, iyayin daliban da aka yi garkuwar da su sunyi kira ga gwamnati ta tabbatar an bawa daliban kulawa da ya dace saboda irin halin damuwa da suka shiga a hannun yan bindigan.

A sanarwar da suka fitar a ranar Laraba, mai dauke da sa hannun Shugaban kungiyar daliban Abdullahi Usman da Sakatariya, Catherine Saleh, sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da tsarin da zai tabbatar dalibai za su yi karatu a yanayi na tsaro.

"Tafiyar ba ta zo karshe ba, tabbas yaranmu za su bukaci taimakon likitoci domin irin halin damuwa da abubuwan tsoro da suka fuskanta yayin da suke tsare," a cewar iyayen.

"Muna kira ga gwamnati ta zage damtse ta bullo da tsarin tabbatar da tsaro wadda zai karfafawa iyaye gwiwa su tura yaransu makaranta, domin idan aka cigaba da barin makarantun babu tsaro, da dama ba za su yarda yaransu su cigaba da zuwa makaranta ba."

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel