Mutanen Gari Sun Ƙona Ƴan Bindiga Uku Ciki Har da Mace a Sokoto

Mutanen Gari Sun Ƙona Ƴan Bindiga Uku Ciki Har da Mace a Sokoto

- Fusatattun matasa a ƙaramar hukumar Goronyo na jihar Sokoto sun halaka yan bindiga uku ciki har da mace

- Ƴan bindigan sunyi yunkurin kai hari ne wani Rugar Fulani su sace shanu cikin dare amma Fulanin suka kama su

- Fulanin sun mika su hannun ƴan banga da safe amma da labari ya kai kunnen matasa sai suka tafi ofishin ƴan bangan suka hallaka su

- Rahotanni sun ce macen da ke cikin ƴan bindigan ne ta fusata matasan inda ta ce musu ba yau aka fara kamata ba kuma za a sake ta

Fusatattun matasa sun kashe wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yayin da suka yi yunkurin kai hari a Goronyo a ranar Laraba, Daily Trust ta ruwaito.

Matasan sun kuma ƙona ofishin ƴan banga da aka fara ajiye wadanda ake zargin.

Yan bindigan sun zo wani Rugar Fulani da ke wajen Goronyo cikin dare domin su sace shanu amma mutanen suka yi fito-na-fito da su suka kama uku cikinsu.

Mutanen Gari Sun Ƙona Masu Garkuwa Uku Ciki Har da Mace a Sokoto
Mutanen Gari Sun Ƙona Masu Garkuwa Uku Ciki Har da Mace a Sokoto. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Gumi Ya Faɗa Mana Gaskiya, Yana Tare Da Ƴan Ta’adda Ne Ko Ƴan Nigeria, Adamu Garba

"Mutanen a shirye suke. Harsashi baya ratsa su. Sun dakile harin kuma suka kama uku cikin yan bindigan suka mika su hannun ƴan banga da safe, in ji wani mazaunin garin.

"Da labarin ya isa wurin matasan mu, sun taru sun tafi ofishin ƴan banga da aka ajiye su a Goronyo.

"Kalaman da ke fitowa bakin ƴar bindigan ya fusata su inda ta ke cewa ba yau aka fara kamata ba kuma ta san za a sake ta.

"Wannan ne ya ɓata musu rai, suka fi karfin ƴan bangan suka cinnawa ofishin wuta.

"Daya daga cikin wanda ake zargin ya mutu a ofishin yan bangan, macen da ɗayan na mijin sunyi yunkurin tserewa amma aka kama su aka kashe su aka ƙona gawarsu," a cewar wani ganau.

KU KARANTA: Mutanen Unguwa a Kano Sun Takawa Masu Garkuwa da Mutane Birki

Shugaban ƙaramar hukumar, Abdulwahab Yahya ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce jami'an tsaro suna sintiri domin tabbatar da doka da oda.

A cewarsa, ƴan bindiga sun dade suna sace shanu a yankin duk da jami'an ƴan sanda 60 da ke garin.

Kakakin ƴan sandan Sokoto, ASP Sanusi Abubakar shima ya tabbatar da afkuwar harin amma ya ce ba shi da cikakken bayani a lokacin haɗa wannan rahoton.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164