'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Jarida, Sunyi Garkuwa da Matafiya da Dama a Katsina

'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Jarida, Sunyi Garkuwa da Matafiya da Dama a Katsina

- Ƴan bindiga sun halaka ɗan jarida, Ibrahim Ɗankabo sun kuma sace wasu mutane da dama a Katsina

- Rahotannin daga yankin ya nuna cewa ƴan bindigan sun harbe ɗan jaridar ne a yayin da ya tafi kaiwa makwabciyarsa ɗauki

- A ɓangarenta, rundunar yan sandan jihar Katsina ta bakin kakakinta ta ce bata da labarin afkuwar lamarin

An kashe wani mai aikin daukar hoto a sashen labarai na karamar hukumar Jibia, Ibrahim Dankabo, ranar Litinin yayin da yan bindiga suka yi garkuwa da mutane, rahoton Premium Times.

Yan ta'addan kuma sun yi garkuwa da matafiya da yawa a yankin, a cewar wata majiya.

'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Jarida, Sunyi Garkuwa da Matafiya da Dama a Katsina
'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Jarida, Sunyi Garkuwa da Matafiya da Dama a Katsina. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Jonathan Ya Yi Jinjina Ga Tsohon Mai Gidansa Ƴar’Adua Shekaru 11 Bayan Rasuwarsa

Wani shugaban yankin, Gide Suleiman, ya shaidawa Premium Times cewa an harbe Dankabo a Kukar-Babangida a karamar hukumar Jibia inda yake rayuwa, lokacin da ya ji ihun wata makwociyar sa lokacin da ake yunkurin garkuwa da mutane.

Yan bindigar sun yi awon gaba da matar wadda mahaifiyar wani mai sarautar gargajiya ce a Kasar Niger, a cewar majiyar.

Kuma, wasu mazauna yankin sun ce maharan sun yi garkuwa da matafiya da dama akan titin Katsina-Jibia wanda da yawan su yan garin Magamar Jibia ne.

KU KARANTA: Gumi Ya Faɗa Mana Gaskiya, Yana Tare Da Ƴan Ta’adda Ne Ko Ƴan Nigeria, Adamu Garba

"Jami'an tsaro suna nan amma yan bindiga suna cin karen su babu babbaka. Jami'an tsaro basa jin kukan mu. Kuma an dauke tankar yakin su guda daya, kusan wata biyu yanzu," inji wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaye sunan sa saboda tsaro."

Mai magana da yawun yan sandan Katsina ya ce bai samu labarin harin na Jibia ba.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel