Mun shawo kan yan bindiga da suka sace daliban Greenfield, ba zasu kashesu ba: Sheikh Gumi

Mun shawo kan yan bindiga da suka sace daliban Greenfield, ba zasu kashesu ba: Sheikh Gumi

- Sheikh Ahmad Gumi ya karbi bakuncin iyayen daliban FCFM Afaka

- Daliban makarantar fasahar gandun dajin sun samu yanci ranar Laraba

- Iyayen sun janye maganarsu na cewa Gumi ya hada su da wani wanda ya karbi N800,000 hannunsu

Sheikh Ahmad Gumi ya ce yan bindigan da sukayi garkuwa da daliban jami'ar Greenfield a Kaduna sun fasa kashesu kamar yadda sukayi barazana ranar Litinin.

Za ku tuna cewa a ranar Litnin, shugaban yan bindigan ya ce idan ba'a biya N100m ba zasu kashe daliban ranar Talata.

Amma a ranar Alhamis yayin karban bakuncin iyayen daliban Afaka da aka ceto jiya, Malamin addinin ya ce yanzu haka suna tattaunawa don ceto daliban jami'ar Greenfield.

Ya ce samun nasarar ceto daliban Afaka ya kara musu karfin gwiwa wajen tattaunawa da yan bindigan, rahoton Daily Trust.

"Har yanzu muna tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da daliban jami'ar Greenfield. Ka san sun yi barazanar kashesu gaba daya a wata rana amma bayan maganar da mukayi musu, sun sauko daga wannan ra'ayi," yace.

"Saboda muna godiya sun fasa kisan. Kuma muna tattaunawa da su."

Ya kara da cewa yan bindigan na kai wadannan hare-hare ne don bakantawa gwamnati rai, amma sun hakan ta hanyar kai hari makarantun gwamnati da sace dalibai.

DUBA NAN: Ba zamu taba yarda wani ya shigo da Masara daga waje ba, gwamnan CBN

Mun shawo kan yan bindiga da suka sace daliban Greenfield, ba zasu kashesu ba: Sheikh Gumi
Mun shawo kan yan bindiga da suka sace daliban Greenfield, ba zasu kashesu ba: Sheikh Gumi Hoto: Dr Ahmad Gumi
Asali: UGC

KU KARANTA: Muna hasashen za'ayi ambaliya a jihohi 28 bana, Ministan Ruwa ya lissafo su

A bangare guda, Shahrarren Malamin addini, Dr Ahmad Mahmud Gumi, ya bada nasa fatawar kan hukuncin biyan yan bindiga masu garkuwa da mutane kudin fansa don su saki mutum.

Wannan ya biyo bayan fatawar Limamin Masallacin tarayya, Farfesa Ibrahim Maqari.

Amma Sheikh Ahmad Gumi a Tafsirin da gudanar ranar Laraba a jihar Kaduna, ya bayyana cewa kuskure ne haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel