‘Yan gudun hijira na taimaka wa ‘yan ta’addan Boko Haram wurin kai hari a Ajiri

‘Yan gudun hijira na taimaka wa ‘yan ta’addan Boko Haram wurin kai hari a Ajiri

- Ana zargin 'yan gudun hijira da taimaka wa ‘yan ta’addan Boko Haram wurin kai hari a garin Ajiri da ke karamar hukumar Mafa, jihar Borno

- Harin da yan ta'addan suka kai garin a ranar Litinin ya yi sanadiyar kashe ‘yan sa kai 15, yan farar hula 10 da kuma sojoji biyar

- An kuma tattaro cewa mayaƙan ƙungiyar ISWAP na kai ziyara ƙauyen da tsakar dare

Rahotanni sun kawo cewa ana zargin wasu ‘yan gudun hijira a garin Ajiri da ke ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno da taimaka wa wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne wajen kaddamar da hari a garin.

PR Nigeria ta ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun yi awon gaba da motoci biyar sannan suka kashe ‘yan sa kai 15, yan farar hula 10 da kuma sojoji biyar a harin da suka kaddamar a ranar Litinin.

KU KARANTA KUMA: Zargin juyin mulki: Manyan hafsoshin tsaro sun sake alkawarin biyayya ga FG, sun bayyana sabbin dabaru

‘Yan gudun hijira na taimaka wa ‘yan ta’addan Boko Haram wurin kai hari a Ajiri
‘Yan gudun hijira na taimaka wa ‘yan ta’addan Boko Haram wurin kai hari a Ajiri Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da motoci biyar tare da kashe ƴan sa kai 15 da farar hula 10 da sojoji 5 a harin da suka kai ranar Litinin.

Garin Ajiri na da nisan kilomita 20 daga garin Dikwa na jihar Borno.

Maharan a cewar wasu majiyoyin soji, sun kai mamaya Ajiri, sun kai hari kan wasu yan farar hula da ‘yan sa kai.

Sannan sai suka yi ƙoƙarin shiga wani sansanin sojoji a yanki amma dakarun ba su ba su dama ba, inda suka yi musayar wuta da ‘yan bindigar.

Jaridar ta bayyana cewa garin Ajiri bai taba fuskantar harin ‘yan bindiga ba sai da gwamnati ta tsugunar da wasu ‘yan gudun hijira a garin.

Bincike ya gano cewa wasu daga cikin ‘yan gudun hijrar iyalan manyan kwamnadojin Boko Haram ne kuma suna ganawa da ‘ya’yansu da a yanzu suka zama mayaƙan ƙungiyar da ke aiki a yankin Tafkin Chadi.

KU KARANTA KUMA: Yar'Adua Bayan Shekaru 11: Abubuwa 6 Game da Marigayi Tsohon Shugaban Najeriya

Haka kuma, an gano cewa mayaƙan ƙungiyar ISWAP na kai ziyara ƙauyen da tsakar dare.

A wani labarin Ahmad Gumi, fitaccen Malamin addinin Islama, ya musanta sanin komai a kan N800,000 da aka biya domin a sako daliban makarantar Afaka da aka sace a jihar Kaduna.

A watan Maris ne 'yan bindiga suka kai hari kwalejin gandun daji dake Afaka a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna suka sace dalibai 39.

Amma kuma tuni aka sako 10 daga cikin daliban inda guda 29 aka sako su a ranar Laraba, 5 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel