Mbaka Bai Bata Ba: Murna Ya Lullube Mabiya Fasto Mbaka Bayan Sake Bayyanarsa

Mbaka Bai Bata Ba: Murna Ya Lullube Mabiya Fasto Mbaka Bayan Sake Bayyanarsa

- Jita-jita sun kau yayin da Fasto Mbaka ya bayyana bayan zanga-zangar da aka yi da zargin ya bata

- Ya fito a wata mota, in da magoya bayansa suka runtuma cikin farin ciki da ganinsa yayin da ya bayyana

- An ruwaito cewa, wasu sun yi zanga-zanga a jihar Enugu suna nuna damuwarsu da batar Faston

An yi zaman murna a jihar Enugu ranar Laraba bayan da Daraktan ruhaniya na Adoration Ministry dake Enugu, Ejike Mbaka, ya sake bayyana bayan damuwar rashin sanin inda yake ya haifar da rudani a jihar.

Lokacin da Mbaka ya dawo a cikin mota ‘yan mintoci kadan bayan karfe 2 na yamma, an ga magoya bayansa suna ihu 'Father Mbaka, Oh! barka da dawowa gida !. "

KU KARANTA: Felicia Adebola, Marubuciyar da Ta Rubuta Taken Alkawarin Najeriya ta Mutu

Mbaka Bai Bata Ba: Murna Ya Lullube Mabiya Fasto Mbaka Bayan Sake Bayyanarsa
Mbaka Bai Bata Ba: Murna Ya Lullube Mabiya Fasto Mbaka Bayan Sake Bayyanarsa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Babban malamin na addinin kirista daga baya ya fito daga motar don nuna murna ga magoya bayansa.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa an yi zanga-zanga a Enugu kan inda Mbaka yake.

KU KARANTA: An Kame Tsohuwa Mai Shekaru 80 Da Jikarta Da Laifin Sayar Da Hodar Iblis

A wani labarin, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta ce ba ita ta ke tsare da malamin addinin Kirista Rev. Fr. Ejike Mbaka ba.

Kakakin hukumar DSS, Peter Afunnaya ne ya bayyana haka a wani sakon tes da aka aika wa jaridar The PUNCH a ranar Laraba.

“Mbaka ba ya tare da DSS, don Allah,” Afunnaya ya rubuta a martaninsa ga wakilin Punch a tambayar da ya yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel