Iyayen Daliban Afaka Sun Ba Gumi Hakuri, Sun Ce Ba Shi Da Alaka Da Batun Fansar N800k

Iyayen Daliban Afaka Sun Ba Gumi Hakuri, Sun Ce Ba Shi Da Alaka Da Batun Fansar N800k

- Iyayen daliban Afaka sun karyata matar da ta yi ikrarin alakanta Sheikh Gumi da fansar N800,000

- Kungiyar ta ce matar ba ta daya daga cikin masu wakiltar kungiyar iyayen yaran da aka sace

- Hakazalika Sheikh Gumi ya musanta zargin, ya kuma siffanta kalaman matar da shirme zalla

Wasu iyayen daliban da aka sace na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya dake Afaka, jihar Kaduna, sun nemi afuwa ga Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama, kan “zargin karya” da ake yi masa.

A watan Maris, 'yan bindiga sun kai hari kwalejin da ke karamar hukumar Igabi suka yi awon gaba da daliban, amma an kubutar da 172 daga cikinsu, inda 39 ke hannunsu.

Daga cikin 39 din da ke hannun 'yan bindiga, 10 sun sake kubuta.

Da take magana a ranar Talata, yayin zanga-zanga a majalisar kasa don sakin ‘ya’yansu, daya daga cikin iyayen ta yi zargin cewa Gumi ya nuna musu wani Bafulatani mai suna Ahmed, wanda ya karbi Naira 800,000 daga wurinsu.

KU KARANTA: An Kame Tsohuwa Mai Shekaru 80 Da Jikarta Da Laifin Sayar Da Hodar Iblis

Iyayen Daliban Afaka Sun Ba Gumi Hakuri, Sun Ce Ba Shi Da Alaka Da Batun Fansar N800k
Iyayen Daliban Afaka Sun Ba Gumi Hakuri, Sun Ce Ba Shi Da Alaka Da Batun Fansar N800k Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Amma a wata sanarwa a ranar Laraba, wanda Abdullahi Usman da Catherine Saleh, shugaba da sakatare na kungiyar iyayen da abin ya shafa suka sanya wa hannu, sun ce ba a biya fansa ta hanyar Gumi ba kuma maganar ta farko daga dayansu ba ta da tushe.

“Muna so mu bayyana a bayyane cewa ikirarin bashi da asali a zahiri. Duk da cewa matar da ke cikin faifan bidiyon tana da yaro a hannun 'yan bindiga, amma ikirarin nata ba gaskiya bane.

"Matar ba memba ce a kwamitin da ke wakiltar iyayen da abin ya shafa ba kuma ba ta yi magana a madadin iyaye ba,” inji su.

“Tabbas, Kungiyar da aka Sace yaransu ba ta taba tattara kudi ba ga Gumi ko wani ta hannun malamin addinin Islaman ba a kowane lokaci.

“Don haka muka nisanta kanmu daga bayanin. Kwamitin ya dauki maganar a matsayin abin takaici da kuma shagala da ba dole ba a jajircewarta na ganin an sako yaransu wadanda a yanzu suka kwashe kwanaki 56 a tsare.

Hakanan, Gumi, wanda aka sani da ke da damar ganawa da wasu 'yan bindigan, ya shaida wa TheCable cewa zargin "shirme ne" kuma ba shi da masaniya kan maganar.

KU KARANTA: Mbaka Bai Bata Ba: Murna Ya Lullube Mabiya Fasto Mbaka Bayan Sake Bayyanarsa

A wani labarin, Dalibai 27 na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya, Afaka, jihar Kaduna an sake su. Daya daga cikin mutanen da suka karbi daliban ya tabbatar wa jaridar Daily Trust labarin.

Ya ce kwamitin tattaunawa na Sheikh Abubakar Gumi ne ya taimaka wajen sakin tare da goyon baya daga tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Daliban na daga cikin mutane 37 da aka sace kusan watanni biyu da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel