Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Saki Dalibai 27 Na Kwalejin Noma Dake Kaduna

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Saki Dalibai 27 Na Kwalejin Noma Dake Kaduna

- 'Yan bindiga sun saki daliban Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji, Afaka dake jihar Kaduna da aka sace

- Rahotanni sun bayyana cewa, Sheikh Gumi tare da Tsohon shugaban kasa Obasanjo ne suka taka rawa wajen sakin daliban

- A baya dai Gwamna El-Rufa'i ya ki amincewa da biyan kudin fansan da 'yan bindiga suka nema na N500m

Dalibai 27 na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya, Afaka, jihar Kaduna an sake su.

Daya daga cikin mutanen da suka karbi daliban ya tabbatar wa jaridar Daily Trust labarin.

Ya ce kwamitin tattaunawa na Sheikh Abubakar Gumi ne ya taimaka wajen sakin tare da goyon baya daga tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Daliban na daga cikin mutane 37 da aka sace kusan watanni biyu da suka gabata.

KU KARANTA: Felicia Adebola, Marubuciyar da Ta Rubuta Taken Alkawarin Najeriya ta Mutu

Da Dumi-Dumi: An saki daliban kwalejin noma da gandun daji na Kaduna
Da Dumi-Dumi: An saki daliban kwalejin noma da gandun daji na Kaduna Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Bayan biyan kudin fansa daga iyaye da shugabannin makarantar, 'yan bindigan sun saki 10 kawai daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su.

Tun da farko wadanda suka sace su sun nemi Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba su kudin fansa har Naira miliyan 500 amma Gwamna Nasir El-Rufai ya yi watsi da batun tattaunawar, yana mai cewa 'yan bindiga sun cancanci a kashe su.

KU KARANTA: Mbaka Bai Bata Ba: Murna Ya Lullube Mabiya Fasto Mbaka Bayan Sake Bayyanarsa

A wani labarin, Daya daga cikin daliban da aka sace a jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna ya kubuta daga hannun 'yan bindiga.

Duk da cewa har yanzu ‘yan sanda da hukumomin gwamnati ba su tabbatar da hakan ba, mahaifiyar daliban, Lauritta Attahiru ta tabbatar da sakin danta ga gidan Talabijin na Channels, a ranar Talata.

Amma duk da haka ta ki bayar da cikakken bayani game da yadda aka saki dan nata kuma an biya fansa ko a'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel