Gwamnatin Buhari Ta Taya Iyayen Daliban Jami'an Greenfield Jimamin Sace Yaransu
- Gwamnatin tarayya ta bayyana matukar damuwa da halin da iyayen daliban jami'ar Greenfield ke ciki
- Gwamnatin ta bayyana da cewa, ta hada kai da gwamnatin jihar Kaduna don kubutar da daliban jami'ar
- Hakazalika ta bayyana cewa, ya kamata 'yan Najeriya su hada kai don yakar lamarin ta'addanci a kasar
Gwamnatin Tarayya a ranar Talata ta ce tana tare da damuwar iyayen daliban da aka sace na Jami'ar Greenfield dake Kaduna.
Wannan na zuwa ne kwanaki 15 bayan da wasu ‘yan bindiga suka afkawa jami’ar Greenfield da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a karamar hukumar Chikun, suka saci dalibai da dama.
Zuwa yanzu, 'yan bindigan sun kashe biyar cikin daliban sannan suka yi barazanar kashe 17 da suka rage a hannunsu matukar ba a ba su kudin fansa na Naira miliyan 100 da babura 10 ba.
Fadar shugaban kasa ta wallafa a shafin Twitter ta ce tana tare da bakin cikin da iyayen wadanda abin ya shafa ke ciki, kuma za ta yi aiki tare da Gwamnatin Jihar Kaduna don kawo karshen wannan mummunan lamarin.
KU KARANTA: An Kama 'Yan Bindiga 12 Da Suka Yi Garkuwa Da Ma'aikatan FRSC 26 a Nasarawa
“Muna matukar bakin ciki da bakin cikin iyayen daliban da aka sace a Jami’ar Greenfield.
"Gwamnatin Tarayya ta hanyar amfani da sojoji da hukumomin leken asiri suna aiki don tallafa wa Gwamnatin Jihar Kaduna don kawo karshen wannan mummunan lamarin ba tare da sake rasa rayukan wadanda ba su ji ba basu gani ba.
“Za mu tabbatar da cewa an yi kyakkyawan nasara a kan ta'addanci, sannan kuma a hukunta dukkan 'yan bindiga da masu aikata ta’addancin da ke addabar rayukan jama’a da al’ummomi.
"Wannan lokaci ne da yakamata dukkan ‘yan Najeriya su hada kai, ba tare da la’akari da addini, kabilanci ko bangaranci ba - kan yaki da wani babban mugun makiyi,” Fadar Shugaban kasar ta fada a daren Talata.
KU KARANTA: Matsalar Tsaro Laifin Gwamnatocin Jihohi Ne, Ba Na Buhari Ba, Lai Mohammed Ga PDP
A wani labarin, Iyayen daliban da aka sace na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji Afaka da ke Jihar Kaduna sun mamaye harabar Majalisar Tarayya, Abuja, suna zanga-zanga, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Masu zanga-zangar wadanda suka hada da membobin kungiyar Dalibai (SUG) na makarantar na nuna alhininsu kan abin da suka bayyana da sakacin gwamnatin jihar da Gwamnatin Tarayya wajen ganin an sako daliban.
Sun rera wakokin hadin kai tare da nuna alluna dauke da bukatar a hanzarta ceto daliban.
“Ilimi hakkinmu ne! Tsaro hakkinmu ne! 'Yanci hakkinmu ne!, A sako daliban Afaka 29!” Iyaye da daliban suna rera waka yayin da suke tafiya zuwa Majalisar Kasa.
Asali: Legit.ng