Matsalar Tsaro Laifin Gwamnatocin Jihohi Ne, Ba Na Buhari Ba, Lai Mohammed Ga PDP

Matsalar Tsaro Laifin Gwamnatocin Jihohi Ne, Ba Na Buhari Ba, Lai Mohammed Ga PDP

- Lai Mohammed ya mai da martani kan jam'iyyar PDP dake zargin gwamnatin Buhari da yin sake da lamarin tsaro

- Ya bayyana cewa, ba laifin gwamnatin tarayya bane halin da ake ciki, laifi ne na gwamnatocin jihohi ciki har da na PDP

- Ya kuma caccaki taron manema labarai da jam'iyya da cewa ba komai bane taron face wasa kawai da suka shirya

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya nemi jam’iyyar PDP da ta ga laifin gwamnatocin jihohi, ciki har da wadanda mambobin jam’iyyar ke shugabanta, a kabubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

A cewarsa, bindiganci da ta'addancin masu satar mutane ba laifin gwamnatin tarayya bane, Channels Tv ta ruwaito.

Shugabannin PDP sun yi taron manema labarai a ranar Litinin, inda suka nuna rashin amincewarsu kan irin halin rashin tsaro da ake ciki a kasar tare da neman gwamnatin tarayya ta magance matsalolin gaba daya.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Saki Wani Dalibin Jami'ar Greenfield ta Kaduna da Aka Sace

Matsalar Tsaro Laifin Gwamnatocin Jihohi Ne, Ba Na Buhari Ba, Lai Mohammed Ga PDP
Matsalar Tsaro Laifin Gwamnatocin Jihohi Ne, Ba Na Buhari Ba, Lai Mohammed Ga PDP Hoto: fmic.gov.ng
Asali: Twitter

Mista Mohammed, memba ne na jam’iyya mai mulki ta APC, ya ce abin takaici ne yadda jam’iyyar adawa ba ta fahimci kokarin da wannan gwamnati mai ci ke yi a kan lamarin ba ciki har da taron zauren garin da aka gudanar a Kaduna inda aka tsara wani shiri na matakai goma.

Ya ce taron manema labarai na PDP ba komai bane face wasa kawai kuma ya kara zargin jam’iyyar da kokarin siyasantar da batutuwan da suka shafi tsaron kasa.

KU KARANTA: Mazauna da Masu Shaguna Sun Tsere Yayin Da Tankar Mai Ta Fadi a Abuja

A wani labarin, Iyayen daliban da aka sace na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji Afaka da ke Jihar Kaduna sun mamaye harabar Majalisar Tarayya, Abuja, suna zanga-zanga, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Masu zanga-zangar wadanda suka hada da membobin kungiyar Dalibai (SUG) na makarantar na nuna alhininsu kan abin da suka bayyana da sakacin gwamnatin jihar da Gwamnatin Tarayya wajen ganin an sako daliban.

Sun rera wakokin hadin kai tare da nuna alluna dauke da bukatar a hanzarta ceto daliban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel