Iyayen Daliban da Aka Sace a Kaduna Sun Mamaye Bakin Majalisar Tarayya Dake Abuja

Iyayen Daliban da Aka Sace a Kaduna Sun Mamaye Bakin Majalisar Tarayya Dake Abuja

- Iyayen daliban da aka sace a Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji a Kaduna sun fita zanga-zanga

- Sun hallara a bakin Majalisar Tarayya a Abuja don nuna alhininsu ga rashin kubutar da daliban

- Hotunan iyayen da wasu mambobin kungiyar dalibai sun bayyana a bakin Majalisar Tarayya

Iyayen daliban da aka sace na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji Afaka da ke Jihar Kaduna sun mamaye harabar Majalisar Tarayya, Abuja, suna zanga-zanga, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Masu zanga-zangar wadanda suka hada da membobin kungiyar Dalibai (SUG) na makarantar na nuna alhininsu kan abin da suka bayyana da sakacin gwamnatin jihar da Gwamnatin Tarayya wajen ganin an sako daliban.

Sun rera wakokin hadin kai tare da nuna alluna dauke da bukatar a hanzarta ceto daliban.

KU KARANTA: Bill Gates Ya Ce Bar Wa Yara Kudi da Yawa Ba Alheri Ba Ne, Ya Bayyana Gadon 'Ya'yansa

Iyayen Daliban da Aka Sace a Kaduna Sun Mamaye Bakin Majalisar Tarayya
Iyayen Daliban da Aka Sace a Kaduna Sun Mamaye Bakin Majalisar Tarayya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

“Ilimi hakkinmu ne! Tsaro hakkinmu ne! 'Yanci hakkinmu ne!, A sako daliban Afaka 29!” Iyaye da daliban suna rera waka yayin da suke tafiya zuwa Majalisar Kasa.

Masu zanga-zangar tun da farko sun hallara a Unity Fountain sannan suka zarce zuwa harabar Majalisar Dokoki inda jami'an tsaro suka hanasu shiga babbar hanyar.

A ranar 11 ga watan Maris 2021, aka sace dalibai 39 daga gidajen kwanansu a kwalejin.

Ya zuwa yanzu an saki dalibai goma daga cikinsu yayin da sauran ke hannun 'yan bindigan.

Kalli hotunan zanga-zangar:

Iyayen Daliban da Aka Sace a Kaduna Sun Mamaye Bakin Majalisar Tarayya
Iyayen Daliban da Aka Sace a Kaduna Sun Mamaye Bakin Majalisar Tarayya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Iyayen Daliban da Aka Sace a Kaduna Sun Mamaye Bakin Majalisar Tarayya
Iyayen Daliban da Aka Sace a Kaduna Sun Mamaye Bakin Majalisar Tarayya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Iyayen Daliban da Aka Sace a Kaduna Sun Mamaye Bakin Majalisar Tarayya
Iyayen Daliban da Aka Sace a Kaduna Sun Mamaye Bakin Majalisar Tarayya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari Za Ta Gurfanar Da Mutane 400 Masu Tallafawa Boko Haram

A wani labarin, Shugaban kungiyar na kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya nada Abu Muhammad a matsayin sabon Amirul Jaysh 'Kwamandan Yaki', ga bangaren da yake jagoranta bayan kashe tsohon Kwamanda, Abu Fatimah.

PRNigeria ta tattaro cewa Shekau da kansa ya harbe Abu Fatimah, a makon da ya gabata, bisa zargin cin amanar mazhabar su.

Wata majiya ta bayyana cewa wasu manyan kwamandoji biyu suma 'Hatsabibi' Shekau ya kashe su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel