An Kama 'Yan Bindiga 12 Da Suka Yi Garkuwa Da Ma'aikatan FRSC 26 a Nasarawa

An Kama 'Yan Bindiga 12 Da Suka Yi Garkuwa Da Ma'aikatan FRSC 26 a Nasarawa

- Rundunar 'yan sanda ta yi nasarar cafke wasu da ake zargi da kitsa sace ma'aikata FRSC 26 a Nassarawa

- Rundunar ta bayyana cewa, ta gudanar da bincike na tsawon watanni bakwai kafin daga bisani ta kame su

- Ta kuma shaida cewa, 'yan bindigan sun hana mazauna yankin barci saboda aikata manyan laifukan fashi

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Nasarawa ta cafke wasu gungun mutane 12, wadanda ake zargi da shirya makarkashiyar sace jami’ai 26 na Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa da ke cikin jihar watanni bakwai da suka gabata.

A ranar Litinin, 14 ga Satumbar, 2020, an kai hari kan jami’an FRSC 26, wadanda ke tafiya a cikin motocin bas biyu daga jihohin Sakkwato da Kebbi a shirinsu na horo a Kwalejin FRSC da ke Udi, Abuja, a mahadar Udege da Titin Mararaban-Udege da misalin karfe 8 na safe.

Wata majiyar ‘yan sanda ta shaida wa wakilin jaridar Punch cewa biyu daga cikin masu garkuwan sun fito ne daga Sakkwato, biyu daga Kebbi, biyu daga Zamfara, uku daga Kano, biyu daga Filato da daya daga jihohin Binuwai.

KU KARANTA: Nasarorin APC a Shekaru 6 Sun Zarce na PDP a Shekaru 16, in ji Yahaya Bello

An Kama 'Yan Bindiga 12 Da Suka Yi Garkuwa Da Ma'aikatan FRSC 26 a Nasarawa
An Kama 'Yan Bindiga 12 Da Suka Yi Garkuwa Da Ma'aikatan FRSC 26 a Nasarawa Hoto: twimg.com
Asali: UGC

"Binciken da rundunar 'yan sanda ta Jihar Nasarawa ta yi a watanni bakwai da suka gabata ya kai ga cafke gungun mambobi 12 da suka kitsa satar," in ji shi.

Majiyar ta bayyana cewa wadanda aka kaman kuma sune ke da alhakin sace mata biyu na tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Nasarawa, Aliyu Tijani, wadanda aka sake su bayan biyan kudin fansa na N5m.

'Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da jikokin babban basaraken garin Udege a karamar hukumar Nasarawa kuma sun sake su ne bayan sun karbi kudin fansa na N10m.

Majiyar ta kuma bayyana cewa, tun lokacin da aka sace jami'an na FRSC, tana kan bakanta na tabbatar da cewa an kama 'yan bindigan, wadanda suka addabi mazauna jihar tare da fuskantar fushin doka.

Majiyar ta kara da cewa "sashin yaki da satar mutane na rundunar a karkashin jagorancin CSP Anietie Eyoh ya sami nasarar zakulo 'yan bindigan a garin Nyanya, da ke cikin karamar hukumar Karu ta jihar, lokacin da suke kokarin tserewa daga hannun 'yan sanda,".

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Ranham Nansel, ya bayyana cewa kafin a kama su, 'yan bindigan sun hana mazauna jihar barci ba dare ba rana saboda aikata ta'addanci.

“Rundunar 'yan sanda ta Nasarawa tana farin ciki da cewa wadannan ‘yan bindiga, da ke addabar mazauna jihar, a karshe jami’anmu sun kama su. Za mu ci gaba da yin komai a cikin ikonmu har sai jihar ta 'yantu daga duk wani nau'i na rashin tsaro,” inji shi.

Nansel ya yi kira ga jama'a da su taimaka wa 'yan sanda ko yaushe da bayanai masu amfani da zai taimaka musu wajen yi wa mutane aiki da kyau.

KU KARANTA: Ku Bayyana Masu Kitsa Kifar da Gwamnatinku, Dattawan Arewa Ga Gwamnatin Buhari

A wani labarin, Daya daga cikin daliban da aka sace a jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna ya kubuta daga hannun 'yan bindiga.

Duk da cewa har yanzu ‘yan sanda da hukumomin gwamnati ba su tabbatar da hakan ba, mahaifiyar daliban, Lauritta Attahiru ta tabbatar da sakin danta ga gidan Talabijin na Channels, a ranar Talata.

Amma duk da haka ta ki bayar da cikakken bayani game da yadda aka saki dan nata kuma an biya fansa ko a'a. Read more: https://hausa.legit.ng/1414449-da-dumi-dumi-yan-bindiga-sun-saki-wani-dalibin-jamiar-greenfield-ta-kaduna-da-aka-sace.html

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.