Ku Bayyana Masu Kitsa Kifar da Gwamnatinku, Dattawan Arewa Ga Gwamnatin Buhari

Ku Bayyana Masu Kitsa Kifar da Gwamnatinku, Dattawan Arewa Ga Gwamnatin Buhari

- Kungiyar Dattawan Arewa ta caccaki zargin da gwamnatin Buhari ke yi na cewa ana kitsa kifar da ita

- Kungiyar ta ce babu amfanin fada wa 'yan Najeriya lamarin, matukar ba mataki gwamnati za ta dauka ba

- Hakazalika ta bayyana cewa, kalaman gwamnati ba komai bane face kokarin tsoratar da 'yan kasa kawai

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta zargi Fadar Shugaban kasa da tsoratar da ’yan Najeriya da kalaman zagon kasa.

Da yake tsokaci game da kararrakin da aka nuna game da zargin yunkurin kifar da Shugaba Muhammadu Buhari, Daraktan Yada Labarai na kungiyar, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya nemi gwamnati mai ci da ta magance matsalolin da kasar ke fuskanta.

NEF, a ranar Talata, ta shaida wa Daily Trust cewa babu wata fa’ida a fada wa ’yan Najeriya cewa wasu 'yan kasa da ba a ambata sunayensu ba suna shirya kifar da shugabanci ta hanyar da ba ta dace da demokradiyya ba a cikin kasar nan.

KU KARANTA: Nasarorin APC a Shekaru 6 Sun Zarce na PDP a Shekaru 16, in ji Yahaya Bello

Ku Bayyana Masu Kitsa Kifar da Gwamnatinku, Dattawan Arewa Ga Gwamnatin Buhari
Ku Bayyana Masu Kitsa Kifar da Gwamnatinku, Dattawan Arewa Ga Gwamnatin Buhari Hoto: theeagleonline.com.ng
Asali: UGC

NEF ta kuma bayyana cewa, yakamata Fadar Shugaban kasa ta iya amfani da hanyoyin da take da su don magance lamarin ba wai fada wa 'yan kasa ba.

Baba-Ahmed ya kalubalanci Fadar Shugaban kasa da ta ambaci makircin da ta ce ana daukar wasu shugabannin kabilu da kuma kabilun da ake zargi suke yi.

Baba-Ahmed ya ce: “Zagon kasa laifi ne, tayar da hankali laifi ne kuma cin amana ma laifi ne. Me yasa Fadar Shugaban Kasa ko DSS ke gaya mana cewa akwai mutanen da ke cikin wadannan ayyukan? Me suke son jama'a suyi da bayanan?

"Sun gaza har sau biyu; da farko dai, sun kasa rufe kofar da ke bada wadannan nau'ikan abubuwan idan sun wanzu, dalilin aikata abinda suke aikatawa kenan sannan kuma sun kasa aiwatar da doka.

“Zan iya cewa mun tattauna da wasu kungiyoyi, mun tattauna batutuwan da suka shafi kasa. Hakkinmu kenan; babu wani abu da ya saba doka a yin hakan kuma na tabbata sauran kungiyoyi suna yin haka.

"Amma sanda kuka jefa irin wannan zargin ga wani wanda ba ku gaya mana ba, wani, wanda kuke adawa da shi a yau, ba ku magance shi ba ne, yana tsundumawa tare da daukar nauyin kungiyoyi masu zaman kansu, ya kamata kuyi mamaki shin kawai kuna amfani da kalmomin ne don tsoratar da yan kasa? ”

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Saki Wani Dalibin Jami'ar Greenfield ta Kaduna da Aka Sace

A wani labarin, Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya nemi jam’iyyar PDP da ta ga laifin gwamnatocin jihohi, ciki har da wadanda mambobin jam’iyyar ke shugabanta, a kabubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

A cewarsa, bindiganci da ta'addancin masu satar mutane ba laifin gwamnatin tarayya bane, Channels Tv ta ruwaito.

Shugabannin PDP sun yi taron manema labarai a ranar Litinin, inda suka nuna rashin amincewarsu kan irin halin rashin tsaro da ake ciki a kasar tare da neman gwamnatin tarayya ta magance matsalolin gaba daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel