Nasarorin APC a Shekaru 6 Sun Zarce na PDP a Shekaru 16, in ji Yahaya Bello

Nasarorin APC a Shekaru 6 Sun Zarce na PDP a Shekaru 16, in ji Yahaya Bello

-Gwamnan jihar Kogi ya bayyana cewa, APC ta cimma nasarorin da PDP bata iya cimmawa ba tsawon shekaru

- Ya kalubalanci nasarorin PDP da cewa, cikin shekaru shida APC ta cimma sama da na PDP a shekaru 16

- Hakazalika ya bayyana bukatar hada kai don magance matsalar tsaro ba wai siyasantar da lamarin ba

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a ranar Talata ya ce jam'iyyar APC mai mulki ta cimma nasarorin da suka zarce na jam'iyyar PDP a shekaru 16.

Bello, ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a shirin Sunrise Daily, ya ce jam’iyyarsa ta isar da kyakkyawan shugabanci ga ’yan Najeriya.

“A takaice, APC ta cimma abin da ya wuce abin da PDP ta cimma a cikin shekaru 16 da suka yi suna mulki a Najeriya,” in ji shi yayin da yake magana daga Fadar Gwamnatin Jihar Kogi da ke Lokoja.

“Nasarorin APC a yau cikin shekaru shida sun fi nasarorin shekaru 16 da suka yi suna mulki. Kididdigar na nan. Za mu tunatar da ‘yan Najeriya game da inda APC ta gaji Najeriya da kuma inda muke a yau.”

KU KARANTA: Karin Bayani: Boko Haram Sun Dira Bauchi, Sun Mamaye Kananan Hukumomi Hudu

APC ta cimma abubuwan da PDP ta kasa ta shekaru 16, Yahaya Bello
APC ta cimma abubuwan da PDP ta kasa ta shekaru 16, Yahaya Bello Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Tun bayan komawa ga mulkin dimokiradiyya a shekarar 1999 PDP ke rike da madafun iko, har zuwa 2015 lokacin da APC ta kore ta.

Dan takarar shugaban kasa na APC a wancan lokacin kuma mai ci yanzu, Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki kan alkawura guda uku - Yaki da rashin tsaro, gyara tattalin arziki da magance rashawa.

Biyo bayan sakonnin sa rai shekaru shida da suka gabata, 'yan Najeriya sun zabi gwamnatin APC tare da imanin cewa abubuwa za su gyaru.

Gwamnan ya kuma yi magana game da tabarbarewar rashin tsaro a kasar, inda ya yi kira ga dukkan 'yan Najeriya da su ba da hadin kai wajen magance matsalar maimakon sanya siyasa a kalubalen tsaro.

Game da yanayin tsaro a jihar Kogi, gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na fatattakar masu aikata laifuka.

KU KARANTA: Mai Sana'ar Yankan Farcen da ke Samun Sama da N45,000 a Wata

A wani labarin, Babban malamin darikar Katolika Fr Ejike Mbaka ya bukaci jam’iyyar APC, da kada ta bata lokaci wajen aiwatar da barazanar da ta ke yi na kai rahotonsa ga Paparoma, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Mbaka na mayar da martani ne ga Yekini Nabena, Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC wanda a cikin wata sanarwa ya ke kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ko dai ya sauka ko kuma a tsige shi saboda kalubalen da ake fuskanta a yanzu rashin tsoron Allah ne.

Mbaka ya yi magana ne game da barazanar tare da wasu batutuwa da ya gabatar a makon da ya gabata yayin hudubarsa a ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel