Bill Gates Ya Ce Bar Wa Yara Kudi da Yawa Ba Alheri Ba Ne, Ya Bayyana Gadon 'Ya'yansa

Bill Gates Ya Ce Bar Wa Yara Kudi da Yawa Ba Alheri Ba Ne, Ya Bayyana Gadon 'Ya'yansa

- Bill Gates ya bayyana adadin kudaden da yaransa za su gada daga dinbin dukiyarsa da ya tara

- Ya bayyana karara cewa, bar wa yara dukiya da yawa ba alheri bane, kuma yana sukar haka

- Bill Gates dai shine na hudu cikin wadanda suka fi kudi a duniya da ya mallaki makudan kudade

Bayan takardun saki na Bill da Melinda Gates sun bayyana cewa ma'auratan ba su taba samun matsala ba, mutane da yawa suna mamakin yadda ma'auratan, tare da jarin dala biliyan 130, za su raba kadarorinsu.

Gates, mutum na hudu da ya fi kudi a duniya, ya yi magana a baya game da yadda kowanne cikin yaransa uku za su gaji kusan dala miliyan 10 na dukiyarsa, inji rahoton jaridar SUN.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari Za Ta Gurfanar Da Mutane 400 Masu Tallafawa Boko Haram

Bill Gates Ya Ce Bar Wa Yara Kudi da Yawa Ba Alheri Ba Ne, Ya Bayyana Gadon 'Ya'yansa
Bill Gates Ya Ce Bar Wa Yara Kudi da Yawa Ba Alheri Ba Ne, Ya Bayyana Gadon 'Ya'yansa Hoto: gettyimages.com
Asali: Getty Images

Lokacin da aka tambaye shi game da jita-jita cewa zai bar wa 'ya'yansa uku - Jennifer, Rory, da Phoebe - dala miliyan 10 kowannensu yayin zamansa da Reddit AMA a shekarar 2013, Gates ya bayyana cewa hakan don amfaninsu ne.

"Babu shakka ina ganin bar wa yara makuddan kudade ba alheri ba ne a gare su," in ji shi, jaridar Punch ta ruwaito.

Shi da Melinda suna da yara uku kuma sun kafa Gidauniyar Bill da Melinda Gates a shekarar 2000 don magance manyan batutuwan duniya da yawa.

Ma'auratan sun ba da gudummawar dala biliyan 45 ta hanyar gidauniyar tun lokacin da aka kafa ta, ciki har da dala biliyan 1.75 don yaki da Korona.

KU KARANTA: Nasarorin APC a Shekaru 6 Sun Zarce na PDP a Shekaru 16, in ji Yahaya Bello

A wani labarin, Bill Gates, attajirin duniya kuma wanda ya kafa kamfanin kwamfuta na Microsoft ya sanar da shirinsa na rabuwa da mai dakinsa Belinda.

Bill da Melinda sun sanar da labarin ne a shafukansu na Twitter a ranar Litinin inda suka ce sun dauki wannan matakin ne bayan nazari sosai.

Ma'auratan sun dade suna jagorantar ayyuka da dama na taimakon jama'a a sassan kasashen duniya daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel