Boko Haram: Shekau Ya Sheke Wani Babban Kwandansa, Ya Nada Sabon Kwamanda

Boko Haram: Shekau Ya Sheke Wani Babban Kwandansa, Ya Nada Sabon Kwamanda

- Shugaban kungiyar Boko Haram Shekau ya hallaka wasu kwamandojinsa bisa zargin saba wa akidarsa

- An ruwaito cewa, Shekau da kansa ya harbe kwamandan tare da wasu sauran mayakansa mutum biyu

- Daya daga cikin wadanda Shekau ya kashe, da ne ga wani shahararren dan kasuwa dake garin Bama

Shugaban kungiyar na kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya nada Abu Muhammad a matsayin sabon Amirul Jaysh 'Kwamandan Yaki', ga bangaren da yake jagoranta bayan kashe tsohon Kwamanda, Abu Fatimah.

PRNigeria ta tattaro cewa Shekau da kansa ya harbe Abu Fatimah, a makon da ya gabata, bisa zargin cin amanar mazhabar su.

KU KARANTA: Idan Ba Za Ka Iya Ba Ka Ba da Wuri, ECWA Ta Bukaci Buhari Ya Yi Murabus

Boko Haram: Shekau Ya Sheke Wani Babban Kwandansa, Ya Nada Sabon Kwamanda
Boko Haram: Shekau Ya Sheke Wani Babban Kwandansa, Ya Nada Sabon Kwamanda Hoto: bbc.com
Source: UGC

Wata majiya ta bayyana cewa wasu manyan kwamandoji biyu suma 'Hatsabibi' Shekau ya kashe su.

Majiyar ta kara da cewa "Bayan wani rikici na cikin gida, Shekau ya kashe Abu Fatima, wani Kwamandansa kuma Amirul Fi'ya, wanda da ne ga fitaccen dan kasuwar Bama, Alhaji Modu Katakauma,"

KU KARANTA: Buhari Bai da Damu da Halin Da ’Yan Najeriya Ke Ciki Ba, PDP Ta Caccaki Buhari

A wani labarin, An kama wasu ma'aikatan gwamnati da aikata fashi da makami a Zamfara, a cewar Gwamnatin Jihar, Channels Tv ta ruwaito.

A cewar wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Magaji Dosara ya sanya wa hannu a ranar Laraba, ma'aikatan gwamnatin suna daga cikin 35 aka kama kuma ake zargin 'yan bindiga ne a Gusau, babban birnin jihar.

"Abin mamaki ne cewa, duk wadanda ake zargin 35 an kama su ne a Gusau, babban birnin jihar kuma wasu daga cikinsu ma'aikatan gwamnati ne," in ji sanarwar.

"Don haka Gwamnatin Jiha ta nuna farin ciki kan kamun bindiga 35 da ke firgita mutane a cikin garin Gusau."

Source: Legit.ng

Online view pixel