Gwamnatin Buhari Za Ta Gurfanar Da Mutane 400 Masu Tallafawa Boko Haram

Gwamnatin Buhari Za Ta Gurfanar Da Mutane 400 Masu Tallafawa Boko Haram

- Biyo bayan kame wasu bata-gari dake tallafawa Boko Haram, za a gurfanar dasu nan ba da dadewa ba

- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, za ta gurfanar da akalla mutane 400 da ta kama dumu-dumu da laifin

- Sai dai, kotuna a fadin Najeriya na garkame saboda yajin aikin da suke ciki tun a watan Afrilu

Gwamnatin tarayya za ta gurfanar da wadanda ake zargi su 400 da aka cafke da laifin tallafawa ‘yan kungiyar Boko Haram da 'yan bindiga, Jaridar The Cable ta ruwaito.

An kama wadanda ake zargin ne a wani samamen hadin gwiwa daga hukumomin leken asirin tsaro (DIA), da sashin tsaro na farin kaya (DSS), da sashin tattara bayanan kudi na Najeriya (NFIU) da kuma Babban Bankin Najeriya (CBN).

An kama su a Kano, Borno, Abuja, Lagos, Sokoto, Adamawa, Kaduna da Zamfara.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da aiwatar da binciken a shekarar 2020.

KU KARANTA: Nasarorin APC a Shekaru 6 Sun Zarce na PDP a Shekaru 16, in ji Yahaya Bello

Gwamnatin Buhari Za Ta Gurfanar Da Mutane 400 Masu Tallafawa Boko Haram
Gwamnatin Buhari Za Ta Gurfanar Da Mutane 400 Masu Tallafawa Boko Haram Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jerin mutane 957 da ake zargi wadanda suka hada da masu gudanar da ayyukan canjin kudi (BDC), masu aikin hakar gwal da masu sayarwa, da kuma wasu ‘yan kasuwa ana ci gaba da aiwatar da bincike akansu.

Wasu daga cikin ma’aikatan canjin kudi da aka kama sun hada da Baba Usaini, Abubakar Yellow (Amfani), Yusuf Ali Yusuf (Babangida), Ibrahim Shani, Auwal Fagge, da Muhammad Lawan Sani, mai sayar da gwal.

Umar Gwandu, mai magana da yawun Abubakar Malami, babban lauyan tarayya (AGF), a ranar Litinin, ya ce tuni an shirya laifukan da suka shafi ta'addanci kan wadanda ake zargin yayin da ake ci gaba da bincike.

Ko da yake kakakin ya ki ba da karin bayani, amma ya ce gurfanar da wadanda ake zargin “za ta fara nan ba da dadewa ba."

Sai dai, dukkan kotuna a fadin kasar suna rufe tun daga ranar 6 ga watan Afrilu saboda yajin aikin da kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya (JUSUN) ke yi a duk fadin kasar.

KU KARANTA: Karin Bayani: Boko Haram Sun Dira Bauchi, Sun Mamaye Kananan Hukumomi Hudu

A wani labarin, Akalla mutum daya farar hula ya rasa ransa yayin da wasu biyar suka jikkata lokacin da wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka yi yunkurin kutsawa cikin garin Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala-Balge da ke jihar Borno, in ji majiyar tsaro.

Lamarin ya faru ne lokacin da haramtacciyar kungiyar ta mamaye garin Rann da misalin karfe 6:15 na maraice suna harbe-harbe amma suka gamu da turjiya daga sojojin Najeriya.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa sojoji sun yi amfani da bindigoginsu a yayin harin da aka kai lamarin da ya haifar da sakamakon lalata motar bindigogi ta maharan, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.