Yan Najeriya Zasu Sami Kwanciyar Hankali a Mulkin Buhari, Bola Tinubu
- Jagoran jam'iyya mai mulki APC, Bola Tinubu, ya bayyana ƙwarin guiwarsa cewa yan Najeriya zasu samu kwanciyar hankali a ƙarƙashin mulkin Buhari
- Bola Tinubu yace shugaban ƙasa Buhari ba zaiso a cigaba da kashe al'ummarsa ba kuma ba zaiso ana sace su ba
- Yace jam'iyyar APC tasan sanda wannan ƙalubalen tsaron ya fara kuma ba zata yi ƙasa a guiwa ba har sai ta magance matsalar
Jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana ƙwarin guiwarsa cewa Najeriya zata magance matsalolin tsaron da take fama dasu a yanzun, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Zamu Cire Tallafin Man Fetur, Gwamnatin Tarayya Tayi Bayani
Yayin da yake jawabi a wurin lakcar tafsirin watan Ramadana wanda ya gudana ranar Lahadi a jihar Lagos, Tinubu yace yan Najeriya zasu sami kwanciyar hankali da zaman lafiya a ƙarƙashin mulkin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari ya karɓi ragamar mulkin ƙasar nan ne a shekarar 2015 kan alƙawurra uku; Magance matsalar tsaro, farfaɗo da tattalin arziki, da kuma gyara yanayin shugabanci.
Sai-dai shekara shida kenan bayan ya samu nasara kan jam'iyyar PDP, wanda hakan ya kawo karshen shakarunta 16 a kan mulki, matsalar tsaro sai ƙara taɓarɓarewa take a ƙarƙashin mulkin gwamnatin APC.
Amma jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, na ganin har yanzun akwai alamun abubuwa zasu dai-daita nan gaba.
KARANTA ANAN: Gwamnonin Arewa Sun Bayyana Matsayarsu a Kan Zargin Da Akewa Sheikh Pantami
Tinubu yace:
"Munsan lokacin da matsalar ta fara amma bamu son bada uzuri, wannan gwamnatin tana aiki tuƙuru, yan Najeriya zasu sami kwanciyar hankali da farin ciki."
"An samu juyin demokaradiyya, dole sai mun ɗakkota daga tushe, mu cigaba da yin hakuri da juna kuma mu nunawa juna soyayya matuƙar muna son mu kai ga nasara."
Jagoran APC na ƙasa ya ƙara da cewa Shugaban ƙasa ba zai so ana kashe al'ummarsa ba kuma ba zaiso ana sace su ba.
Hakanan kuma Bola Tinubu ya gargaɗi waɗanda ke saka siyasa a cikin matsalolin tsaron da ƙasar nan ke fama dasu.
Ya bayyana cewa APC tasan sanda ƙalubalen tsaronnan ya fara, kuma ba zata karaya ba har sai ta magance shi.
A wani labarin kuma Kashi 70% na matasan Najeriya yan zaman kashe wando ne, Inji NOA
Hukumar NOA ta bayyana cewa kashi 60% na mutanen Najeriya matasa ne, kuma aƙalla matasan sun kai miliyan N80m.
Hukumar ta kuma bayyana cewa kashi 70% daga cikin matasa miliyan N80 da Najeriya ke dasu basu da cikakkken aikin yi.
Asali: Legit.ng