Kashi 70% na matasan Najeriya yan zaman kashe wando ne, Inji NOA

Kashi 70% na matasan Najeriya yan zaman kashe wando ne, Inji NOA

- Hukumar NOA ta bayyana cewa kashi 60% na mutanen Najeriya matasa ne, kuma aƙalla matasan sun kai miliyan N80m

- Hukumar ta kuma bayyana cewa kashi 70% daga cikin matasa miliyan N80 da Najeriya ke dasu basu da cikakkken aikin yi

- Daraktan Hukumar yace babu wata ƙasa da ta cigaba batare da taimakon matasa ba

Aƙalla kashi 70% na matasan Najeriya da suka kai 80 miliyan basu da ayyukan yi a wani rahoto da hukumar bada horo NOA ta fitar.

KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: Dalilin Da Yasa JAMB Ta Buɗe Cibiyoyin Dake Maguɗin Jarabawa

Daraktan NOA, Richard Abimiku, shine ya bayyana haka a wani taron kwana ɗaya na ƙarawa juna sani wanda ya gudana a Makurɗi, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Yace Najeriya nada matasa kimanin 80 miliyan wanda sune kashi 60% na gaba ɗaya yawan al'ummar ƙasar.

Ya ƙara da cewa amma babban abun takaicin shine kashi 70% na waɗannan matasan da Najeriya ke dasu basu da tsayayyan aikin yi.

Kashi 70% na matasan Najeriya yan zaman kashe wando ne, Inji NOA
Kashi 70% na matasan Najeriya yan zaman kashe wando ne, Inji NOA Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Abimiku yace cigaban kowace ƙasa a duniyar nan ya ratayane a irin matasan da wannan ƙasar take samarwa.

Richard Abimiku yace:

"Zaka sha mamaki idan kasan cewa adadin matasan Najeriya ya kai 80 miliyan, waɗannan matasan sune kashi 60% na yawan jama'ar Najeriya.

"Amma kashi 70% na waɗannan 80 miliyan ɗin basu da aikin yi. Babu shakka shekarun da yafi kamata a gina rayuwar mutum shine a lokacin da yake matashi."

KARANTA ANAN: Madalla! Daliban Jami’ar FUAM da Aka Sace a Jihar Benuwai Sun Kuɓuta

"Duk wani cigaba na wata ƙasa ya rataya ne a kan matasan da take samarwa, Matasa ne suke kawo cigaba a ƙasa ta hanyoyi da dama, sune suke aikin ƙarfi domin samar da kayayyakin amafani masu inganci."

Ya kuma jinjina wa matasa a kokarin da suke yi na zama da kafafunsu a ɓangarori da dama kamar; ɓangaren wasanni, ilimi, fasahar zamani, Kasuwanci da suransu.

Yace abu ne mai matuƙar muhimmanci a gina matasa su zama masu dogaro da kansu, kuma a taimakesu su rinƙa tunani mai kyau duk da ƙalubalen da suke fuskanta.

A wani labarin kuma Gwamnan Rivers Ya Caccaki APC, Yace Babu Wani Mai Hankali da Zai So APC a 2023

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike , ya caccaki jam'iyya mai mulki da ƙoƙarinta na daƙile shirin gyaran dokokin zaɓe .

Gwamnan yace APC na jin tsoron ayi gyaran ne saboda yan Najeriya sun dawo daga rakiyarta kuma ba zasu zaɓi jam'iyyar ba a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262