Dalilin da Yasa Zamu Cire Tallafin Man Fetur, Gwamnatin Tarayya Tayi Bayani

Dalilin da Yasa Zamu Cire Tallafin Man Fetur, Gwamnatin Tarayya Tayi Bayani

- Gwamnatin tarayya na shirye-shiryen cire tallafin mai nan bada jimawa ba kamar yadda ƙaramin ministan tattalin arziƙin mai ya bayyana

- Ministan yace ba zai yuwu gwamnati ta cigaba da biyan maƙudan kuɗaɗe don tallafawa yan ƙasa amma tallafin baya zuwa garesu.

- Yace baya son bayyana waɗanda ke cinye kuɗin amma wasu tsirarun yan kasuwa ne Kaɗai ke amfana da kuɗin

Gwamnatin tarayya ta ƙara jaddada wa yan Najeriya cewa su shiryawa ƙarin farashin man fetur saboda matsin tattalin arziƙin da ƙasar ke ciki.

KARANTA ANAN: Wasu mazauna Geidam sun bayyana yadda yan Boko Haram ke musu wa'azi bayan sun ƙwace iko

Karamin ministan mai, Chief Timipre Sylva, shine ya bayyana haka ga manema labarai a wajen yaye ɗalibai da basu kyaututtuka a jami'ar Patakwal, jihar Rivers.

Sylva yace nan bada jimawa ba gwamnati zata zare tallafin man fetur, wanda a cewarsa wasu yan kasuwa ne kaɗai ke amfanaa da tallafin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Dalilin da Yasa Zamu Cire Tallafin Man Fetur, Gwamnatin Tarayya Tayi Bayani
Dalilin da Yasa Zamu Cire Tallafin Man Fetur, Gwamnatin Tarayya Tayi Bayani Hoto: @HETimipreSylva
Asali: Twitter

Ministan yace:

"Abun takaici ne idan aka sami ƙarin farashin litar mai, to nan danan zai karaɗe kasuwa kuma bamujin dadin hakan. Musamman shugaban ƙasa baya son cire tallafin amma matsin tattalin arziƙi ya mana illa sosai."

"Shin zamu cigaba da bada tallafin man fetur, wanda talaka baya amfana dashi, amma wasu ɗai-ɗaikun yan kasuwan ƙasar nan kaɗai ke amfana dashi? Bana son in bayyana mutanen dake amfana da tallafin."

KARANTA ANAN: Kashi 70% na matasan Najeriya yan zaman kashe wando ne, Inji NOA

"Yan Najeriya basa amfana da tallafin mai kai tsaye, babban abinda keda alaƙa da yan Najeriya shine kalanzir da mutanen karkara ke amfani dashi wajen girki, sai kuma man fetur da suke mfani dashi wajen tafiye-tafiye. Dukkan waɗannan ba'a ƙayyade farashin su ba na tsawon lokaci."

Sylva ya ƙara da cewa gwamnati zata cigaba da biyan tallafin mai na wani lokaci saboda yanzun ana tattaunawa da masu ruwa da tsaki ne a kan lamarin.

Yace da zarar an kammala tattaunawa da masu ruwa da tsakin, za'a sanar da zare tallafin kai tsaye.

A wani labarin kuma Gwamnan Rivers Ya Caccaki APC, Yace Babu Wani Mai Hankali da Zai So APC a 2023

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike , ya caccaki jam'iyya mai mulki da ƙoƙarinta na daƙile shirin gyaran dokokin zaɓe .

Gwamnan yace APC na jin tsoron ayi gyaran ne saboda yan Najeriya sun dawo daga rakiyarta kuma ba zasu zaɓi jam'iyyar ba a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262