Gwamnonin Arewa Sun Bayyana Matsayarsu a Kan Zargin Da Akewa Sheikh Pantami

Gwamnonin Arewa Sun Bayyana Matsayarsu a Kan Zargin Da Akewa Sheikh Pantami

- Ƙungiyar gwamnonin arewa tayi martani a kan kace-nace da ake tayi kan wasu kalamai da ministan Sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Isa Pantami, yayi a baya

- Gwamnonin sun bayyana cewa basu son a saka su a cikin lamarin, domin a cewarsu basu da alaƙa da irin waɗannan kalaman

- Wasu daga cikin yan Najeriya sun ƙalubalanci Pantami da yin kalamai a baya waɗanda suke nuna yana da tsattsauran ra'ayi

Ƙungiyar gwamnonin arewa (NSGF) ta nesanta kanta da duk wata kalar cece-kuce da wasu yan Najeriya keyi kan kalaman da Ministan Sadarwa Pantami yayi a baya.

KARANTA ANAN: Rashin Tsaro: APC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Gwamnonin PDP

A rahoton da Legit.ng ta tattaro, ƙungiyar gwamnonin arewa sun bayyana cewa ba laifi bane idan Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani ya faɗi ra'ayinsa.

A jawabin ƙungiyar tace Ministan ya wanke kansa inda yayi martani a kan lamarin, kuma martaninsa ba ya buƙatar bincike ko kuma ƙin amincewa domin yayi cikakke bayani.

Gwamnonin Arewa Sun Bayyana Matsayarsu a Kan Zargin Da Akewa Sheikh Pantami
Gwamnonin Arewa Sun Bayyana Matsayarsu a Kan Zargin Da Akewa Sheikh Pantami Hoto @DrIsaPantami
Asali: Twitter

NSGF tace: "Ministan ya fito ya kare kansa, kuma jawabinsa baya buƙatar bincike ko kuma ƙin amincewa."

Hakanan ƙungiyar gwamnonin tace ta gano wani labari da a ke yaɗawa a kafafen sada zumunta domin ɓatawa gwamnonin yankin arewa suna, inda ake yaɗa jita-jitar cewa suna goyon bayan kalaman da Dr. Pantami yayi a baya.

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Zamu Cire Tallafin Man Fetur, Gwamnatin Tarayya Tayi Bayani

Ƙungiyar tayi kira ga al'umma da suyi watsi da duk wani labari da suka gani a na yaɗawa a kafafen sada zumunta domin a ɓata musu suna.

Hakanan, Isa Pantami, yayi zargin cewa duk waɗannan abubuwan dake faruwa akansa shirayayyu ne, kuma an shiryasu ne domin a ɓata masa suna.

A wani jawabi da mai magana da yawun ministan, Uwa Sulaiman, ta fitar ta bayyana cewa akwai wani shirin da suke yi na sakin wani ƙirƙirarren bidiyo a kan Ministan.

A wani labarin kuma Kashi 70% na matasan Najeriya yan zaman kashe wando ne, Inji NOA

Hukumar NOA ta bayyana cewa kashi 60% na mutanen Najeriya matasa ne, kuma aƙalla matasan sun kai miliyan N80m.

Hukumar ta kuma bayyana cewa kashi 70% daga cikin matasa miliyan N80 da Najeriya ke dasu basu da cikakkken aikin yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262