Rashin Tsaro: An Shiga Rudani Yayinda Gwamnan APC Ya Caccaki INEC a Kan Sanar da Ranakun Zaben 2023
- An samu sabani tsakanin Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi da INEC kan sanarwar ranakun zaben 2023
- Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, a ranar Laraba, 28 ga Afrilu ya sanar da ranakun zaben na 2023
- Sai dai kuma, Umahi ya caccaki hukumar zaben kan yin magana game da zaben ana tsaka da rashin tsaro a kasar
David Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, a ranar Juma’a, 30 ga Afrilu, ya far wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), saboda sanar da ranakun da za a gudanar da babban zabe na 2023 ana tsaka da fama da matsalolin tsaro a kasar.
Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, 28 ga watan Afrilu, yayin taron yini guda da aka gudanar don sauraron laifukan zabe na 2021 da kwamitin Majalisar Dattawa kan INEC ya shirya.
KU KARANTA KUMA: El-Rufai Yana Nema Wa Hukumomin Tsaro Kudi, Ya Koka Kan Karuwar Fashi da Makami
Legit.ng ta tattaro cewa Umahi yayi magana ne yayin mika motocin da gwamnatin jihar ta sayo ga hukumomin tsaro da kuma Ebube-Agu, kayan tsaro na kudu maso gabas a masaukin gwamnan, Abakaliki.
Ya ce abin takaici ne yadda hukumar zaben ke magana kan zaben alhalin kasar tana cikin wani hali.
Umahi ya ce:
“Kasar tana fuskantar kalubale yanzu. Ba batun shugaban kasa ko gwamna bane. Wajibi ne dukkan shugabanni su ɗauki nauyi a wannan matakin saboda ba abin da kuke wa’azinsa a cikin jama’a ba ne yayin da muke tunkarar batun cewa dole mu kare makomar yaranmu. Me kuke yi da wannan? ”
Sai dai kuma, mai magana da yawun shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce ranar da za a gudanar da babban zaben na 2023 ya dogara ne da tsarin da INEC ta kafa tun a shekarar 2018.
KU KARANTA KUMA: Zan Yi Duk Me Yiwuwa Don Dawo da Zaman Lafiya da Tsaro a Najeriya – Buhari
Ya ce hukumar ta yanke shawarar hakan ne domin tabbatar da gaskiya, ya kara da cewa babban zaben a Najeriya zai dunga kasancewa a ranar Asabar ta uku ta Fabrairun shekarar zabe.
A wali labarin, yayin da gwamnatocin tarayya da na jihohi ke kokarin magance matsalar rashin tsaro a kasar, David Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, ya bayyana cewa a shirye yake ya sasanta al'amura tare da 'yan fashi.
Da yake magana a ranar Juma’a, 30 ga Afrilu, a Abakiliki, Umahi wanda ya bayyana ‘yan fashin a matsayin “’ya’yanmu” ya ce yana son gano abin da ke damunsu don samar da mafita ga kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta a yanzu.
Asali: Legit.ng