Zan Yi Duk Me Yiwuwa Don Dawo da Zaman Lafiya da Tsaro a Najeriya – Buhari

Zan Yi Duk Me Yiwuwa Don Dawo da Zaman Lafiya da Tsaro a Najeriya – Buhari

- Shugaba Buhari ya yi alkawarin magance matsalolin tsaro na kasar

- A zahiri, shugaban kasar ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don ganin hakan ta faru

- Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da ya yi wata ganawa da majalisar tsaron kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a shirye yake ya yi duk mai yiwuwa don dawo da zaman lafiya da tsaro a kasar.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa dauke da sa hannun mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya) kuma aka ba Legit.ng.

KU KARANTA KUMA: Matasa Sun Ƙona Motocci da Gidajen Mai Garkuwa da Mutane a Kwara

Zan Yi Duk Me Yiwuwa Don Dawo da Zaman Lafiya da Tsaro a Najeriya – Buhari
Zan Yi Duk Me Yiwuwa Don Dawo da Zaman Lafiya da Tsaro a Najeriya – Buhari Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

An ruwaito cewa shugaban kasar ya sha wannan alwashin ne yayin muhimmin taro na Majalisar Tsaro ta Kasa.

Wani bangare na sanarwar ya ce:

"A taron na yau shugaban kasar ya bayyana a sarari cewa yayin da masu tayar da kayar baya, 'yan fashi da masu aikata laifi suke ta’asarsu har yanzu, ba shi da shakku cewa hukumomin tsaron Najeriya da dukkanmu a matsayinmu na kasa za mu shawo kan dukkanin matsalolin tsaro na yau da kullun tare da fatattakar tawagar shaidanu a yankuna daban-daban na kasar.

"Yayin da masu laifin suka ci gaba da gwada nufin gwamnatin Najeriya, Shugaban kasa da Majalisar wadanda suka dage muhimmiyar taron yau har zuwa safiyar Talata don karbar karin bayani daga shugabannin tsaro, an shirya kuma sun yanke shawarar kawo karshen cin zarafin da ake yi wa al'umma da kuma yin duk abin da ya kamata.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Rundunar soji ta sauyawa Operation Lafiya Dole suna

"Mai girma shugaban kasa ya shirya tsaf don daukar kwararan matakai don ra’ayin mutane da kuma kasar Najeriya. Ba za a yi nadama ba har sai an maido da zaman lafiya da tsaro sosai a cikin garuruwanmu."

A baya mun kawo cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar tsaro a fadar Shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya, Abuja.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

Sai Shugaban Ma'aikatan Fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, NSA Manja Janar Babagana Monguno (mai murabus) da kuma wasu ministoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng