'Yan Bindiga' Ya'yan Mu Ne, Na Kan Ji Bakin Ciki Idan Aka Kashesu, Gwamna Umahi Yana Neman Sulhu

'Yan Bindiga' Ya'yan Mu Ne, Na Kan Ji Bakin Ciki Idan Aka Kashesu, Gwamna Umahi Yana Neman Sulhu

- Bayan sanya dokar hana zirga-zirga a Ebonyi kan tabarbarewar rashin tsaro, Gwamna Umahi ya shirya tattauna da 'yan bindiga

- Burin Umahi shine gano dalilin da yasa suke fusata tare da samar da ingantattun hanyoyin magance kalubalen tsaro a yanzu a jihar

- Gwamnan ya umarci shugabannin kananan hukumomi da shugabannin addinai da su gano ‘yan fashin tare da kawo su tattaunawar sulhu

Yayin da gwamnatocin tarayya da na jihohi ke kokarin magance matsalar rashin tsaro a kasar, David Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, ya bayyana cewa a shirye yake ya sasanta al'amura tare da 'yan fashi.

Da yake magana a ranar Juma’a, 30 ga Afrilu, a Abakiliki, Umahi wanda ya bayyana ‘yan fashin a matsayin “’ya’yanmu” ya ce yana son gano abin da ke damunsu don samar da mafita ga kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta a yanzu.

KU KARANTA KUMA: Jerry Gana Ya Yi Barazanar Maka Majalisar Ƙolin Musuluncin Nigeria a Kotu

'Yan Bindiga' Ya'yan Mu Ne, Na Kan Ji Bakin Ciki Idan Aka Kashe su, Gwamna Umahi Yana Neman Tattaunawa
'Yan Bindiga' Ya'yan Mu Ne, Na Kan Ji Bakin Ciki Idan Aka Kashe su, Gwamna Umahi Yana Neman Tattaunawa Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Gwamnan ya bayyana aniyar tasa ne yayin gabatar da motoci kirar Toyota Sienna 40 da manyan motocin daukar kaya guda 20 ga hukumomin tsaro don bunkasa ayyukansu a jihar, NAN ta ruwaito.

Ya ce:

“Ina so na yi magana da ‘yan fashin tare da tallafa masu tunda ba za mu iya ci gaba da kashe kanmu da lalata kayayyakin jama’a ba.

"'Yan fashin yaran mu ne kuma ina bakin ciki idan aka kashe su ko kuma jami'an tsaro."

A cewar Jaridar Premium Times, Umahi ya nemi kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) da shugabannin kananan hukumomi da su bayyana yan fashin kuma su gabatar dasu domin tattaunawa.

Ya ce bayan gano gaskiyar lamarin, za a fara tattaunawa da kuma hanyar ci gaba.

KU KARANTA KUMA: A jihar Kano kadai ake yaki da rashawa kamar EFCC da ICPC, Gwamna Ganduje

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a shirye yake ya yi duk mai yiwuwa don dawo da zaman lafiya da tsaro a kasar.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa dauke da sa hannun mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya) kuma aka ba Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Online view pixel