Sanya Dokar Ta-baci Ba Za Ta Magance Matsalar Tsaro Ba - Masari

Sanya Dokar Ta-baci Ba Za Ta Magance Matsalar Tsaro Ba - Masari

- Gwamna Aminu Bello Masari ya bada shawarar cewa ayyana dokar ta-baci ba za ta kawo karshen matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar ba

- Masari ya ce babu wadatar dakarun soji da za a yi amfani da su wajen ayyana dokar ta-baci a kasar saboda ayyukan da ke gabansu a halin yanzu sun sha musu kai

- Ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis yayin amsa tambayoyin manema labarai bayan ganawarsa da Shugaban Ma’aikatan Fadar shugaban kasa

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bada shawarar cewa sanya dokar ta-baci ba za ta magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta ba.

Masari ya ba da wannan shawarar ne a ranar Alhamis yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai na gidan Gwamnati bayan ganawa da Shugaban Ma’aikata na shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram Ta Kai Hari Kan Sansanin Soji A Borno, Ta Lalata Komai, Cewar Rahoto, Sojoji Sun Maida Martani

Sanya Dokar Ta-baci Ba Za Ta Magance Matsalar Tsaro Ba - Masari
Sanya Dokar Ta-baci Ba Za Ta Magance Matsalar Tsaro Ba - Masari Hoto: BBC.Com
Asali: UGC

Idan za a iya tunawa, majalisar wakilai a ranar Talata ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta sanya dokar ta-baci a bangaren tsaro don magance matsalar rashin tsaro a kasar.

A cewarsa,babu wadatar dakarun soji da za a yi amfani da su wajen ayyana dokar ta-baci a kasar saboda ayyukan da ke gabansu a halin yanzu sun sha musu kai, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Don haka gwamnan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina sanya siyasa a cikin al’amuran tsaro, yana mai cewa samar da tsaro a kasar a wannan mawuyacin hali nauyi ne da rataya a wuyan kowa.

Ya ce ba za a bar Najeriya ta wargaje ba domin hakan na nufin babbar matsala ga nahiyar Afirka baki daya.

Dangane da fargabarsa a kan cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta iya biyan jihohi kasafin kudinsu na watan Mayu ba, Masari ya nemi masu ruwa da tsaki kan lamarin da su yi duk wata mai yiwuwa wajen ganin hakan ba ta faru ba.

KU KARANTA KUMA: Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutu Ranar Litinin Domin Murnar Ranar Ma’aikata

A cewarsa, matukar jihohi da kananan hukumomi za su tsinci kansu cikin rashin samun kasafin kudin wata daga gwamnatin tarayya, hakan na iya kara rura wutar matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar.

A gefe guda, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ba zai bari a samu cigaba na kwarai a Najeriya ba.

A cewar Ganduje, da irin wannan cin hanci da rashawar da akeyi a Najeriya, da kamar wuya a samu cigaba saboda cin hanci yana kashe kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel