Gwamnoni Sun Koka, Sun Nemi Buhari Ya Dauki Mataki Yayinda Aka Sake Kashe Mutum 21

Gwamnoni Sun Koka, Sun Nemi Buhari Ya Dauki Mataki Yayinda Aka Sake Kashe Mutum 21

- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, takwaransa na jihar Neja, Sani Bello da Samuel Ortom na jihar Binuwai sun koka kan lamarin tsaro a kasar

- Gwamnonin sun yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan ya dauki matakin gaggawa domin lamarin na shirin kwacewa

- Sun yi wannan kiran ne a ranar Talata, 27 ga watan Afrilu yayinda aka kashe mutum 21 a fadin kasar

Sanatoci da gwamnoni uku a ranar Talata sun nuna damuwa game da kashe-kashe da sace-sacen mutane a kasar, suna masu rokon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nemi taimakon kasashen waje.

'Yan majalisar, yayin da suke tattaunawa kan wani kudiri kan ayyukan kungiyar Boko Haram a jihar Neja, sun bayyana rashin tsaro a kasar a matsayin abin kunya.

Sanata Sani Musa (All Progressives Congress, Neja ta gabas) ne ya dauki nauyin kudirin.

Gwamnoni Sun Koka, Sun Nemi Buhari Ya Dauki Mataki Yayinda Aka Sake Kashe Mutum 21
Gwamnoni Sun Koka, Sun Nemi Buhari Ya Dauki Mataki Yayinda Aka Sake Kashe Mutum 21 Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: APC Za Ta Yi Mulki Har Bayan 2023, 'Yan Najeriya Suna Son Jam'iyyar Mai Mulki, Inji Tinubu

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum; takwaransa na jihar Neja, Sani Bello da Samuel Ortom na jihar Benuwe, a tattaunawa daban-daban sun yi gargadin cewa rashin tsaro a kasar yana neman fin karfi, jaridar Punch ta ruwaito.

Don haka gwamnonin suka bukaci Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta daukar mataki yayin da aka kashe mutane 21 a fadin kasar a ranar Talata.

Zulum, a wata hira da ya yi da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa a daren Litinin, ya ce ya kamata a fada wa Shugaban kasa gaskiya game da rashin tsaro a kasar.

A nasa bangaren, Ortom ya koka kan harin da makiyaya suka kai yankin Abegana na jihar inda aka kashe mutane bakwai a ranar Talata.

Bello, a wata hira da aka yi da shi a Gidan Talabijin na Najeriya ranar Talata, ya ce Boko Haram na fatattakar mutane daga garuruwan jihar Neja.

An gabatar da rashin tsaro a jihar Neja a gaban majalisar dattijai a ranar Talata yayin da Sanata Musa a cikin kudirinsa ya tabbatar da kalaman gwamnan, yana mai cewa yawancin garuruwan jihar suna karkashin ikon Boko Haram.

Ya ce, “Kimanin garuruwa 42 a fadin kananan hukumomi biyu na Shiroro da Munya sun fada karkashin ikon Boko Haram tare da kimanin mazauna kauyuka 5,000 da suka rasa muhallinsu a cikin kwanaki uku da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Yan Boko Haram sun fara rabawa mutane N20,000 a garin Geidam

“Sun yi garkuwa da mutane da yawa sannan kuma suka kwace matansu daga hannunsu sannan aka hadasu da mambobin kungiyar Boko Haram.

"An kori sansanonin soji uku da ke Allawa, Bassa da Zagzaga a cikin kananan hukumomin biyu sannan maharan sun kashe wasu jami'an tsaro a cikin sabbin hare-haren da suka kai wata daya da ya gabata."

A wani labarin, gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, da takwaran sa na jihar Ribas, Nyesom Wike, sun sanya dokar hana fita a jihohinsu.

Channels TV ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Anambra ta dauki wannan matakin ne bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a wasu garuruwan da abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel