Rashin Tsaro: Gwamnonin Najeriya 2 Sun Saka Dokar Kulle a Jihohinsu

Rashin Tsaro: Gwamnonin Najeriya 2 Sun Saka Dokar Kulle a Jihohinsu

- Gwamna Obiano da Gwamna Wike sun dauki matakan shawo kan matsalolin tsaro da suka dabaibaye jihohinsu

- Gwamnonin biyu sun shawarci mazauna yankin da su bi matakan tsaro da aka sanya a jihohinsu

- Wasu jihohi a yankin kudu maso gabashin kasar na fuskantar hare-hare daga wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba

Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, da takwaran sa na jihar Ribas, Nyesom Wike, sun sanya dokar hana fita a jihohinsu.

Channels TV ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Anambra ta dauki wannan matakin ne bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a wasu garuruwan da abin ya shafa.

KU KARANTA KUMA: Muna Jin Tsoro, Boko Haram Na Iya Mamaye Abuja – Sanatocin Najeriya Sun Koka

Rashin Tsaro: Gwamnonin Najeriya 2 Sun Saka Dokar Kulle a Jihohinsu
Rashin Tsaro: Gwamnonin Najeriya 2 Sun Saka Dokar Kulle a Jihohinsu Hoto: @GovWike, @WillieMObiano
Asali: Twitter

Garuruwan sune Igbariam, Aguleri, Umueri, Nteje, Awkuzu da Umunya.

Sakataren gwamnatin jihar Anambra, Farfesa Solo Chukwulobelu, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa dokar hana zirga-zirgar da ta fara a ranar Litinin, 26 ga Afrilu, ana sa ran za ta kasance tsakanin 7 na yamma zuwa 6 na safe a kowace rana.

A cewar jaridar Vanguard, ya bukaci mazauna jihar da ke zaune a cikin wadannan jerin garuruwa da su yi biyayya ga dokar hana fita.

Farfesa Chukwulobelu ya bayyana cewa jami'an tsaro suna kan tsauraran umarni don aiwatar da dokar hana fita.

Hakazalika, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sanya dokar hana fitar dare a dukkan iyakokin da Ribas ta raba da Abia, Akwa Ibom, Bayelsa, da Imo.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, gwamnan ya dauki matakin ne biyo bayan hare-hare da kashe-kashen jami'an tsaro da yan bindiga suka yi na baya-bayan nan.

Da yake magana a wani shirin da aka watsa a ranar Talata, 27 ga Afrilu, WIke ya bayyana cewa dokar hana zirga-zirgar za ta fara aiki daga ranar Laraba, 28 ga Afrilu, da karfe 8 na dare.

Ya ce:

"Gwamnatin Jihar Ribas ta yanke shawarar takaita zirga-zirgar dare zuwa ciki da fita daga kan iyakokin jihar.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Ka yafewa 'yan Najeriya da suka dinga zaginka, J. Martins ga Jonathan

“Sakamakon haka, an sanya dokar hana zirga-zirgar dare kuma ba a barin wani mutum ko abin hawa shiga da fita daga Jihar Ribas daga karfe 8.00 na dare. zuwa 6.00 na safiya daga gobe (Laraba) 28 ga Afrilu 2021 har zuwa wani lokaci.

"Muna so mu ba da shawara cewa wadanda ke da wata bukata ta daban ko dalilin shigowa ko fita daga jihar dole ne su yi hakan kafin karfe 8.00 na dare lokacin da dokar hana fita za ta fara aiki a kullum."

A wani labarin, a ranar Talata, 27 ga watan Afirilun 2020, 'yan daba a jihar Sokoto sun kone ofishin 'yan sanda dake karamar hukumar Kware ta jihar.

Gungun 'yan daban da suka kunshi matasa, sun isa ofishin 'yan sandan inda suka dinga ihu tare da jaddda cewa akwai wasu wadanda aka kama da laifin garkuwa da mutane amma aka sake su.

'Yan daban sun fi karfin 'yan sandan inda suka rinjayi jami'an tsaron dake gadin ofishin kuma suka koneshi tare da motar DPO da kuma motocin sintiri guda biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel