APC Za Ta Yi Mulki Har Bayan 2023, 'Yan Najeriya Suna Son Jam'iyyar Mai Mulki, Inji Tinubu
- Tsohon gwamnan jihar Legas, Sanata Bola Tinubu na da kwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta ci gaba da rike madafun iko a matakin tarayya bayan zaben 2023
- Tinubu wanda shine shugaban jam'iyyar na kasa yayi wannan bayanin ne bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Tinubu ya gana da shugaban kasar ne tare da wani tsohon shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC, Cif Bisi Akande
Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Bola Tinubu, ya ce ‘yan Najeriya suna kaunar APC kuma tana da damar ci gaba da rike madafun iko a matakin tarayya har bayan 2023.
'Yan Najeriya za su dawo kan layuka don zabar sabbin rukunin masu rike da mukaman gwamnati a dukkan bangarori a zangon farko na shekarar 2023.
KU KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Gwamnonin Najeriya 2 Sun Saka Dokar Kulle a Jihohinsu
Da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da suka yi da Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Kasa, Abuja a daren Litinin, 26 ga Afrilu, Tinubu ya ce:
“Damar da muke da shi tana da haske kamar tauraruwar tsakar dare kuma za mu ci gaba da aiki don inganta Najeriya. Ba za mu iya saka siyasa da hasashe a komai ba, muna da kasar da za mu gina.”
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa tsohon gwamnan na jihar Legas ya kuma yi kira ga dukkan yan kasa masu kyakkyawar manufa da su ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya a yayinda ake tsaka da fuskantar matsalolin tsaro a wasu sassan kasar.
KU KARANTA KUMA: Muna Jin Tsoro, Boko Haram Na Iya Mamaye Abuja – Sanatocin Najeriya Sun Koka
A cewarsa, dole ne dukkan ‘yan Najeriya su ajiye banbancinsu na addini, siyasa, ko na kabilanci sannan su hada kai da jami’an tsaro don shawo kan matsalar.
Jaridar The Nation ta ruwaito Tinubu yana fadin cewa ya je fadar shugaban kasa tare da Cif Akande domin tuntubar shugaba Buhari kan hanyoyin magance matsaloli daban-daban da kasar ke fuskanta, inda ya bukaci dukkan ‘yan Najeriya da su marawa gwamnati baya.
A cewarsa, rashin jin dadin da ake ciki a yanzu ba za a iya cewa na musamman ba ne amma ya kamata a yi tarayya wajen samar da mafita, ta hanyar tuntuba da musayar ra'ayoyi kan yadda za a sauya arzikin kasar.
A wani labarin, a ranar Talata, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙara bayyana buƙatar goyon baya daga ƙasar Amurka da sauran manyan ƙasashe wajen daƙile matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.
Shugaban yace goyon bayan ya zama wajibi domin rashin tsaro a Najeriya sai ya shafi dukkan ƙasashe, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng