Gwamnatin Tarayya Na Kan Sake Fasalin Tsaron Najeriya, in ji Osinbajo

Gwamnatin Tarayya Na Kan Sake Fasalin Tsaron Najeriya, in ji Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, kasar na sake fasalin tsaro

- Ya kuma yi tsokaci kan cewa, Najeriya babbar kasa ce da ayyukan 'yan sanda ba zai isa ba

- Hakazalika ya nemi goyon bayan sarakunan gargajiya da su tallafawa shirin gwamnati na sake fasalin

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa Najeriya za ta iya shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar al’ummar kasar nan, yana mai bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na sake fasalta dukkan tsarin tsaro a kasar.

Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin da ya karbi ziyarar ban girma a fadar shugaban kasa ta mai martaba, Yakanaje Uke, (na jihar Nasarawa), Alhaji Dr. Ahmed Abdullahi Hassan, TVC ta ruwaito.

A cewar Mataimakin Shugaban kasar, “babu wata shakka ko kadan cewa muna fuskantar kalubalen tsaro, amma muna iya shawo kansu. Matsayin jagoranci shine a zauna a yi tunani kan matsalolin.

KU KARANTA: Saura Kiris ’Yan Boko Haram Su Shiga Babban Birnin Tarayya Abuja, in ji Gwamnan Neja

Gwamnatin Tarayya Na Kan Sake Fasalin Tsaron Najeriya, in ji Osinbajo
Gwamnatin Tarayya Na Kan Sake Fasalin Tsaron Najeriya, in ji Osinbajo Hoto: theguardian.ng
Asali: UGC

“Wannan babbar kasa ce, saboda haka aikin 'yan sanda na da matukar wahala. Akwai bukatar mu sake tsara tsarin fasalin tsaro, wanda ke gudana a yanzu.”

Mataimakin shugaban kasar ya bayar da tabbacin cewa kalubalen da ake fuskanta a yanzu zai shirya Najeriya don samun ci gaba mai kyau da kuma girma, yana mai kira ga masarautun gargajiya da su tallafawa tsarin sake fasalin.

A kalamansa: “Na yi imani sosai cewa dalilin da ya sa muke fuskantar halin da muke ciki a yau shi ne saboda a shirya mu don nan gaba.

Osinbajo ya bayyana cewa, idan ba a shiga matsalolin a yanzu ba, zai yi wahala 'yan kasar su fahimci bambanci tsakanin adalci da rashinsa.

KU KARANTA: An Kwamushe Masu Bai Wa ’Yan Boko Haram Bayanai, Ciki Har da Likita a Jihar Neja

A wani labarin, Aminu Masari, gwamnan jihar Katsina, ya ce wasu kalubalen da kasar ke fuskanta wani bangare ne na shiryata ta zama kasa mai karfi, TheCable ta ruwaito.

Masari ya yi wannan batun ne a ranar Litinin lokacin da ya karbi bakuncin wakilai daga majalisar wakilai kan ziyarar ta’aziyya ta gobarar da ta tashi a babbar kasuwar Katsina da kuma majalisar dokoki.

Gwamnan ya ce wasu kasashe sun shiga cikin mawuyacin hali, ya kara da cewa da azama da jajircewa, Najeriya za ta shawo kan duk wata matsala sannan ta kara karfi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel