An Kwamushe Masu Bai Wa ’Yan Boko Haram Bayanai, Ciki Har da Likita a Jihar Neja

An Kwamushe Masu Bai Wa ’Yan Boko Haram Bayanai, Ciki Har da Likita a Jihar Neja

- Gwamnatin jihar Neja ta yi nasarar kame wasu bata-gari dake kai wa 'yan Boko Haram bayanai

- Gwamnatin jihar ta bayyana haka ne tare da cewa cikinsu har da wani likita cikin mutane tara

- A makon nan ne gwamnan jihar ya bayyana cewa, Boko Haram sun kafa tutocinsu a wasu sassan jihar

Gwamnatin jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar Najeriya ta ce ta kama mutum tara da ake zargin masu kai wa Boko Haram bayanai ne.

A cewar mai bai wa gwamnan jihar Neja shawara kan yada labarai, Abdullberqy Ebbo, daya daga cikin mutum tara da aka kama likita ne.

Ya bayyana cewa mutanen sun yi ikirarin bayar da bayanai game da sojoji ga mayakan.

KU KARANTA: Osinbajo Ya Bayyana Hasashensa Ga Ci Gaban Najeriya, Ya Ce Za a Samu Zaman Lafiya

An kwamushe masu bai wa 'yan Boko Haram bayanai, ciki har da likita a jihar Neja
An kwamushe masu bai wa 'yan Boko Haram bayanai, ciki har da likita a jihar Neja Hoto: thenationonlineng.com
Asali: UGC

A baya-bayan nan gwamnatin jihar ta Neja ta bayyana cewa kungiyar Boko Haram ta kafa tuta a wasu kananan hukumomin jihar guda biyu.

Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello wanda ya tabbatar da kasancewar Boko Haram a jihar ya ce mayakan sun kafa tuta ne a kananan hukumomin Kaure da Shiroro.

KU KARANTA: Matsalolin da Najeriya ke fuskanta alamu ne na ci gaba, in ji gwamna Masari

A wani labarin, Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya ce mayakan Boko Haram sun yi kusa da babban birnin kasar., Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana lokacin da ya ziyarci sansanin 'Yan Gudun Hijira a ranar Litinin, gwamnan ya ce 'yan ta'addan sun karbe wani yanki na jihar bayan Gwamnatin Tarayya ta gaza a kokarin samar da tsaro a jihar.

Ya ce ya tuntubi Gwamnatin Tarayya a lokuta daban-daban amma babu wani abu mai amfani da ya fito daga kokarinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel