Da Ɗuminsa: Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana abinda Buhari ya tattauna da sakataren Amurka

Da Ɗuminsa: Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana abinda Buhari ya tattauna da sakataren Amurka

- Shugaba Buhari ya roki ƙasar Amurka da tazo su haɗa ƙarfi da karfe wajen daƙile kalubalen tsaron da Najeriya ke fama dashi

- Shugaban ya roƙi ƙasar da ta duba yuwuwar dawo da hedkwatar taimakawa ƙasashen Africa (AFRICOM) daga ƙasar Germany zuwa nahiyar Africa.

- Buhari yayi wannan roƙon ne a wata tattaunawa da yayi da sakataren Amurka ta hanyar amfani da fasahar zamani

A ranar Talata, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙara bayyana buƙatar goyon baya daga ƙasar Amurka da sauran manyan ƙasashe wajen daƙile matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

Shugaban yace goyon bayan ya zama wajibi domin rashin tsaro a Najeriya sai ya shafi dukkan ƙasashe, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Yan Arewa Zasu Fi Son Bola Tinubu Ya Zama Magajin Buhari

A jawabin da mai baiwa shugaban shawara ta musamman kan yaɗa labari, Mr. Femi Adesina ya fitar, yace shugaban yayi wannan kira ne a yayin tattaunawarsa da sakataren Amurka Mr Anthony Blinken.

Jawabin wanda aka yi wa take da 'Rashin Tsaro: Shugaba Buhari ya roƙi Amurka ta dawo da hedkwatar AFRICOM zuwa africa'

Bayan roƙon Amurka ta taimaka wa Najeriya, shugaba Buhari ya kuma yi kira ga Amurka da ta duba yuwuwar dawo da hedkwatar taimakawa Africa (AFRICOM) zuwa nahiyar ta Africa, kusa da inda zata gudanar da aikinta.

Da Ɗuminsa: Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana abinda shugaba Buhari ya tattauna da sakataren Amurka
Da Ɗuminsa: Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana abinda shugaba Buhari ya tattauna da sakataren Amurka Hoto: @bashirAhmad
Asali: Twitter

Buhari yace:

"Matsalar tsaron da Najeriya ke fama dashi ya kasance babban abin damuwa garemu, kuma yana barazana ga zaman lafiyar yankin Sahara, tsakiya da kuma yammacin Africa, kamar yadda yake tasiri a tafkin Chadi."

KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: Yadda jirgin yaƙin NAF, Boko Haram Suka hallaka sojoji 33 a Mainok

"Saboda karuwar wannan halin, Najeriya da dukkan hukumomin tsaronta na cigaba da ƙoƙarin magance matsalar da kuma gano asalin inda matsalar ta faro."

"Muna matuƙar buƙatar taimako daga kasashe masu tasiri da muhimmanci kamar Amurka saboda duk abinda rashin tsaro a Najeriya zai janyo, to zai shafi dukkan kasashe. Saboda haka akwai buƙatar mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen murƙushe wannan ƙalubalen da Najeriya ke fama dashi.

Shugaban ya kuma taya Blinken murna bisa wannan muƙami da shugaban Amurka ya bashi, ya kuma jinjina wa ƙasar Amurka da warware dokar da gwamnatin baya tayi na hana wasu kasashen musulmai shiga Amurka.

A wani labarin kuma Gwamnatin Kaduna ta faɗi wani abu mai muhimmanci lokacin da taje Ta'aziyyar Ɗaliban Greenfield da aka kashe

Gwamnatin jihar Kaduna ta tura wakilai ƙarkashin jagorancin kwamishinan Ilimin jihar suje su yiwa iyayen ɗaliban jami'ar Greenfield da yan bindiga suka kashe ta'aziyya

A jawabinsa na wajen ta'aziyyar, kwamishi nan Ilimin, Shehu Muhammed, yace gwamnati na nan akan bakarta na babu tattaunawar sulhu tsakaninta da yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel