An Yi Bata-Kashi Tsakanin Sojojin Chadi Da ’Yan Ta’adda, an Kashe Soji 12

An Yi Bata-Kashi Tsakanin Sojojin Chadi Da ’Yan Ta’adda, an Kashe Soji 12

- 'Yan ta'adda masu da'awar Jihadi sun kai hari kan wasu sojojin kasar Chadi inda suka hallaka 12

- An ruwaito cewa, an hallaka 'yan ta'addan 40, saura kuma sun gudu sun bar gawarwakin 'yan uwansu

- Fada tsakanin sojojin na Chadi da 'yan ta'addan ya faru ne da wayewar garin yau, ranar Talata

Fadan da aka gwabza tsakanin sojoji da masu da'awar jihadi a yankin tafkin Chadi a ranar Talata ya yi sanadiyyar rayukan 'yan kasar ta Chadi akalla 12, kamar yadda wani gwamnan lardin ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP.

Mahamat Fadoul Mackaye ya ce an kuma kashe mayakan 40 bayan harin da aka kai kan wani sansanin sojoji a yankin na fadama da kungiyoyin jihadi da suka hada da Boko Haram da ke Najeriya da kuma wani reshe na kungiyar ISWAP suka yi a baya-bayan nan.

"Dakarun tsaron sun mai da martani mai karfin gaske don fatattakar abokan gaba, wadanda suka bar gawarwaki 40 da makamai, amma muna bakin cikin rashin sojoji 12," in ji Mackaye ga AFP ta wayar tarho.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: ’Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Tarayya Dake Ebonyi Wuta

An Yi Bata-Kashi Tsakanin Sojojin Chadi Da ’Yan Ta’adda, an Kashe Soji 12
An Yi Bata-Kashi Tsakanin Sojojin Chadi Da ’Yan Ta’adda, an Kashe Soji 12 Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

'Yan Boko Haram da ISWAP suna kai wa sojoji hari har da fararen hula a yankunan Chadi arewa maso gabashin Najeriya.

Kungiyar ISWAP ta balle daga kungiyar Boko Haram a shekarar 2016 ta kuma zama kungiyar da ta fi karfi, ta fara kai hare-hare a kan sansanonin soja da kuma yi wa sojoji kwanton bauna yayin sace matafiya a wuraren binciken bogi.

Fadan na ranar Talata ya faru ne da wayewar gari tsakanin garuruwan Ngouboua da Kaiga, wadanda ke da nisan kilomita 100 arewa da babban birnin N’Djamena, in ji wani babban jami’in jami’an tsaro, wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Kakakin rundunar sojojin Chadi, Janar Azem Bermandoa Agouna, ya tabbatar da afkuwar harin amma ya ki bada adadin wadanda suka rasa rayukansu lokacin da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tuntube su.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya Na Kan Sake Fasalin Tsaron Najeriya, in ji Osinbajo

A wani labarin, Gwamnatin sojin kasar Chadi ta sanar da nada sabon Firaministan rikon kwarya wanda ya yi takarar shugabancin kasa a zaben da aka yi a wannan watan, BBC ta ruwaito.

An nada Albert Pahimi Padacké bayan mutuwar shugaban kasar Idriss Deby a makon jiya.

Mr Albert Pahimi Padacké ya rike matsayin Firaministan karkashin gwamnatin marigayi Deby kafin daga baya ya soke matsayin a 2018.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.