Matsalolin da Najeriya ke fuskanta alamu ne na ci gaba, in ji gwamna Masari

Matsalolin da Najeriya ke fuskanta alamu ne na ci gaba, in ji gwamna Masari

- Gwamnan jihar Katsina ya bayyana cewa, Najeriya na kan turbar ci gaba du ba da matsalolinta

- Ya yi imanin cewa, duk wata kasa da ta ci gaba dole sai da ta fuskanci matsaloli daban-daban

- Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su dukufa wajen mai do da martabar kasar ba wai zargin juna ba

Aminu Masari, gwamnan jihar Katsina, ya ce wasu kalubalen da kasar ke fuskanta wani bangare ne na shiryata ta zama kasa mai karfi, TheCable ta ruwaito.

Masari ya yi wannan batun ne a ranar Litinin lokacin da ya karbi bakuncin wakilai daga majalisar wakilai kan ziyarar ta’aziyya ta gobarar da ta tashi a babbar kasuwar Katsina da kuma majalisar dokoki.

Gwamnan ya ce wasu kasashe sun shiga cikin mawuyacin hali, ya kara da cewa da azama da jajircewa, Najeriya za ta shawo kan duk wata matsala sannan ta kara karfi.

"Mun yi imanin wasu matsalolin da kasar ke ciki, wani bangare ne na ci gaba," in ji Masari.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya Yi Ganarwar Sirri da Tinubu da Akande

Matsalolin da Najeriya ke fuskanta alamu ne na ci gaba, in ji gwamna Masari
Matsalolin da Najeriya ke fuskanta alamu ne na ci gaba, in ji gwamna Masari Hoto: bbc.com
Asali: UGC

“Duba da tarihi daga sassa daban-daban na duniya, kasashe sun shiga cikin mawuyacin hali kuma sun fito da karfi, hadin kai, azama da manufa.

“Na yi imani, tare da azama da jajircewa, za mu iya shawo kan dukkan matsalolinmu, saboda muna da dama, iyawa, albarkatu na mutane da sauransu, don magance halin da ake ciki yanzu.

"Kuma da yardar Allah, za mu magance su baki daya don amfanin kasarmu da Afirka baki daya."

Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su hada kai su maida hankali wajen magance matsalolin kasar, maimakon zargin laifi ga juna.

Ya kuma bukaci majalisar kasa da ta samar da shugabanci da ake bukata da goyon baya don magance kalubalen kasar.

A karshe ya ce: "Muna da matsayi na dabaru a Afirka dangane da yawan jama'a, albarkatu da kuma karfin ceton al'ummarmu."

KU KARANTA: Daga Malam Daurawa: Mutane 12 da Zasu Iya Shan Azumi a Ramadana

A wani labarin, Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Lahadi ya ce "akwai alkawarin Allah" ga Najeriya kuma kasar za ta zama "gidan zaman lafiya, tsaro da ci gaba irin wanda ba a taba ganin irinsa ba a wannan nahiya da ma ta gaba da ita."

Ya yi wannan bayanin ne lokacin da yake jawabi a wajen babban taron shekara-shekara karo na 108 na Babban Taron Baptist na Najeriya a Jihar Ogun, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Farfesa Osinbajo ya kara da cewa Najeriya "za ta kasance cibiyar ci gaban tattalin arziki da kimiyya na karni na 21," a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa Laolu Akande ya sanya hannu akai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel