Saura Kiris ’Yan Boko Haram Su Shiga Babban Birnin Tarayya Abuja, in ji Gwamnan Neja

Saura Kiris ’Yan Boko Haram Su Shiga Babban Birnin Tarayya Abuja, in ji Gwamnan Neja

- Gwamnan jihar Neja ya bayyana cewa, 'yan Boko Haram na daf da shiga birnin Abuja idan ba a kula ba

- Ya gargadi cewa, tsakanin in da suke yanzu a jihar Neja da Abuja tafiyar awanni biyu ne kacal

- Ya bayyana haka ne yayin da ya ziyarci sansanin 'yan gudun hijira in da ya tarar da mata da dama

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya ce mayakan Boko Haram sun yi kusa da babban birnin kasar., Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana lokacin da ya ziyarci sansanin 'Yan Gudun Hijira a ranar Litinin, gwamnan ya ce 'yan ta'addan sun karbe wani yanki na jihar bayan Gwamnatin Tarayya ta gaza a kokarin samar da tsaro a jihar.

Ya ce ya tuntubi Gwamnatin Tarayya a lokuta daban-daban amma babu wani abu mai amfani da ya fito daga kokarinsa

KU KARANTA: Karin Bayani: An Hallaka Mutane 8 Daga Cikin Wadanda Aka Sace a Coci a Kaduna

Saura Kiris ’Yan Boko Haram Su Shiga Babban Birnin Tarayya Abuja, in ji Gwamnan Neja
Saura Kiris ’Yan Boko Haram Su Shiga Babban Birnin Tarayya Abuja, in ji Gwamnan Neja Hoto: googleapis.com
Asali: UGC

Bello ya yi gargadin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram na kokarin mai da Kaure a karamar hukumar Shirroro da ke jihar ta zama hedikwatarsu kamar yadda suka yi a dajin Sambisa a jihar Borno.

Saboda da haka, ya ce yayin dajin Sambisa ke da nisan kilomita da yawa daga Abuja, tsakanin Kaure da Abuja awanni biyu kawai.

“Na nemi taimakon gwamnatin tarayya amma abin takaici lamarin ya kai ga wannan matakin kuma idan ba a kula ba, hatta Abuja ba za ta tsira ba. Mun dade muna fadin haka amma duk kokarin da ake yi ya zama a banza.”

Da yake jawabi kan yawan 'yan gudun hijirar da ke sansanin, Bello ya ce wasu daga cikinsu sun fara komawa gida yana mai cewa mafi yawansu za su ci gaba da zama a sansanin saboda 'yan ta'adda sun kwace garuruwansu da kauyukansu

A lokacin ziyarar gwamnan, akwai yara 1,447, mata masu ciki 119 da wasu mata 447 a sansanin.

KU KARANTA: An Nada Wanda Idriss Deby Taba Kora a Matsayin Sabon Firaministan Chadi

A wani labarin, 'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram ta kafa tuta a kauyen Kaure da ke Shiroro a karamar hukumar jihar Niger, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Abubakar Sani Bello ne ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci sansanin yan gudun hijira da ke makarantar frimare na IBB da ke kusa da fadar sarki a Minna.

An sauya makarantar frimarin zuwa sansanin yan gudun hijira cikin gaggawa bayan kimanin mutane 5000 sun baro kauyukansu a kananan hukumomin Shiroro da Munya saboda harin yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.