APC ta bayyana lokacin da shugaba Buhari zai yi Maganin Yan ta'adda da masu ɗaukar nauyinsu
- Jam'iyya mai mulki, APC, ta bayyana cewa nan gaba kaɗan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da yan majalisarsa zasu kawo ƙarshen rashin tsaron ƙasar nan
- APC ta faɗi haka ne a wani jawabi data fitar ɗauke da sa hannun sakataren ta, John Akpanudoedehe
- Yace jam'iyyar APC ba zata yi wasa da rayukan yan ƙasa ba ta hanyar saka siyasa a cikin lamarin tsaro
A ranar Litinin, Jam'iyyar APC tace bada jimawa ba shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa zasu yi maganin duk wani dake da hannu a ƙaruwar matsalar tsaron ƙasar nan.
Ta ce wannan yanayin na rashin tsaro abun damuwa ne matuƙa, saboda haka jam'iyyar ba zata saka siyasa a lamarin da ya shafi rayuwar yan Najeriya ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Yan Bindiga sun kai hari Zariya, Sun yi Awon gaba da mata da Yara
Wannan na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da APC ta fitar, wadda aka yiwa take da "Ya zama wajibi mu haɗa kai domin magance rashin tsaro-APC" ɗauke da sa hannun sakataren jam'iyyar, John Akpanudoedehe.
Akpanudoedehe yace:
"Matsalolin tsaro a ƙasar nan da suka haɗa da ta'addancin Boko Haram, yan Bindiga, masu satar mutane, ɓarayin shanu da kuma na kwanan nan kai hari a kan hukumomin tsaro a wasu jihohi."
"Waɗannan sune gaskiyar matsalolin dake addabar Najeriya, kuma APC ba zata saka siyasa a cikin matsalar data shafi rayuwan yan ƙasa ba, da kuma cigaba da kasancewar Najeiya ƙasa guda ɗaya."
"A matsayin jam'iyyar mu dake rike da madafun iko, mun maida hankali ne wajen gano masu ɗaukar nauyin waɗannan munanan ayyukan, kuma a kamo su domin su fusakanci hukunci."
KARANTA ANAN: NAF ta bayyana Matakin da zata ɗauka kan zargin da ake mata na kai hari ta sama kan sojoji a Mainok
Ya ƙara da cewa jam'iyyar APC na jajantawa duk wanda wannan matsalar ta shafa kuma tana kira ga yan Najeriya su haɗa kansu wajen ganin an warware matsalolin.
Sakataren ya ƙara da cewa: "Sai muna zaune lafiya ne sannan zamu iya morar ayyukan walwala da gwamnati ta kawo kamar irinsu gyaran hanyoyin da suka lalace, gina sabbin gidaje da kuma titin jirgin ƙasa da ake yi, wanda zai haɗa garuruwa da yawa a ƙasar."
Daga ƙarshe jam'iyyar ta roƙi hukumomin tsaro da su binciko duk wani mai hannu a taimakawa yan ta'adda, sannan kuma a tabbatar an hukunta shi kamar yadda doka ta tanadar.
A wani labarin kuma Tsohon Sufetan Yan Sanda Ya Bayyana Hanyar da Gwamnati Zata Bi Ta Magance Matsalar Tsaro
Wani tsohon sufetan yan sandan ƙasar nan ya baiwa gwamnatin tarayya shawarar yadda zata yi ta daƙile matsalar tsaron ƙasar nan da jami'an yan sanda kawai.
Ya ce babu isassun yan sanda a ƙasar nan idan ka kwatanta da yawan jama'ar da Najeriya ke dasu.
Asali: Legit.ng