Pantami: NSCIA Ta Caccaki CAN, Tace Tsohon Ministan Kirista Ya Bayar da Belin Wanda Ya Kafa Boko Haram Sau 3

Pantami: NSCIA Ta Caccaki CAN, Tace Tsohon Ministan Kirista Ya Bayar da Belin Wanda Ya Kafa Boko Haram Sau 3

- NSCIA ta shawarci kungiyar CAN da ka da ta kawo rikicin addini a Najeriya

- Kungiyar kiristocin ta nemi gwamnatin tarayya da ta kori Pantami saboda kalaman da ya yi a baya kan Boko Haram

- Sai dai NSCIA, ta bayyana kiraye-kirayen da kungiyar CAN ta yi a matsayin makirci

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta bayyana ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami a matsayin mutum mai son zaman lafiya da rikon amana.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa akwai kiraye-kiraye da ake yi wa ministan na ya yi murabus saboda kalaman da ya yi a baya game da Boko Haram da sauran kungiyoyin ta'addanci.

KU KARANTA KUMA: Tashe-tashen Hankula Sun Karade Ko'ina a Najeriya Yayin Da Wasu 'Yan Bindiga Suka Kashe 'Yan Sanda 9 a Kebbi

Pantami: NSCIA Ta Caccaki CAN, Tace Tsohon Ministan Kirista Ya Bayar da Belin Wanda Ya Kafa Boko Haram Sau 3
Pantami: NSCIA Ta Caccaki CAN, Tace Tsohon Ministan Kirista Ya Bayar da Belin Wanda Ya Kafa Boko Haram Sau 3 Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa Samuel Ayokunle, shugaban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) na kasa, ya kuma yi kira da a gudanar da bincike kan takaddamar da ke tattare da ministan.

Da yake magana a ranar Litinin, 26 ga Afrilu, a cikin wata sanarwa da Salisu Shehu, mataimakin sakatare-janar na NSCIA ya fitar, kungiyar ta Islama ta ce wadanda ke kiran a sanya wa Ministan takunkumi, ciki har da kungiyar CAN, sun fita ne don makirci.

Shehu ya ce NSCIA na iya yin kira ga gwamnati da ta kama wani fitaccen tsohon minista da ya bayar da belin Mohammed Yusuf, marigayi wanda ya kafa kungiyar Boko Haram, sau uku.

Sanarwar ta zo kamar haka:

“Tare da duk wadannan bayyanannun nasarorin da ya bayar da gudummawa ga ci gaban Najeriya da gina kasa da kuma samar da zaman lafiya, ya zama abin takaici kwarai da gaske cewa shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya na kasa zai shiga cikin kungiyar wawaye marassa karfi da ke tallata karya da karairayi ga mai girma minista.”

Ya ce akwai bukatar a tunatar da shugaban CAN na kasa cewa NSCIA a koyaushe tana taka tsan-tsan kan batutuwan da suka shafi daidaikun masu rike da mukaman siyasa sai dai lokacin da ya zama dole kamar irin na yanzu.

KU KARANTA KUMA: Rikici Ya Barke, an Bindige Kwamishina da Wasu Mutane a Jihar Imo

Shehu ya ci gaba da cewa idan har da NSCIA ta kasance mai son nuna wariya da kuma nuna kiyayya da cutarwa, da ta nemi gwamnatin Najeriya a shekarun 2008 da 2009 da ta kama tare da bincikar wani fitaccen ministan Kirista wanda ya taba bayar da belin marigayi shugaban na Boko Haram lokacin da jami'an tsaro suka kama shi na karshe.

A gefe guda Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama, ya ce al’ummar kasar za su yi nadama idan aka tsige Isa Pantami, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani daga mukaminsa, TheCable ta ruwaito.

Yawancin 'yan Najeriya da kungiyoyi suna ta rokon Shugaba Muhammadu Buhari ya tsige Pantami bayan bidiyo da aka nuna a shekarun 2000 sun sake bayyana inda aka ga ministan yana goyon bayan Al-Qaeda da Taliban.

Pantami, duk da haka, ya sake tunani game da tunaninsa na baya-bayan nan game da kungiyoyin ta'addancin, yana mai cewa matsayinsa a lokacin ya dogara ne da fahimtarsa lokacin da yake saurayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel