Waiwaye: Yadda El-Rufai Ya Nemi Jonathan Ya Tattauna Kan Sakin 'Yan Matan Chibok

Waiwaye: Yadda El-Rufai Ya Nemi Jonathan Ya Tattauna Kan Sakin 'Yan Matan Chibok

- Yayinda Gwamna Nasir El-Rufai ke ci gaba da hawa dokin naki kan batun tattaunawa da yan bindiga a jihar Kaduna, an waiwayi yadda ya goyi bayan haka a mulkin Jonathan

- An tattaro cewa a lokacin da mayakan Boko Haram suka sace 'yan matan Chibok, gwamnan ya kasance dan gaba cikin masu kira ga tsohon shugaban kasar da ya ceto su

- Harma ya goyi bayan bin duk hanyar da ta dace don ceto yaran koda kuwa ta hanyar tattaunawa da mayakan ne

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi watsi da zabin tattaunawa da 'yan bindiga, yana mai cewa sun cancanci a kashe su.

'Yan fashin, wadanda suka sace daliban Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta tarayya (Afaka) Kaduna, sun nemi gwamnati ta ba su N500 miliyan kudin fansa amma gwamnan ya yi biris.

Goma daga cikin dalibai 39 da aka sace a makarantar sun samu 'yanci bayan iyayensu sun tattauna da' yan fashin kai tsaye.

Waiwaye: Yadda El-Rufai Ya Nemi Jonathan Ya Tattauna Kan Sakin 'Yan Matan Chibok
Waiwaye: Yadda El-Rufai Ya Nemi Jonathan Ya Tattauna Kan Sakin 'Yan Matan Chibok Hoto: @elrufai
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: Pantami: NSCIA Ta Caccaki CAN, Tace Tsohon Ministan Kirista Ya Bayar da Belin Wanda Ya Kafa Boko Haram Sau 3

A makon da ya gabata, wasu mutane dauke da makamai suka afka wa jami’ar Greenfield da ke Kaduna inda suka yi awon gaba da dalibai da dama amma duk da haka gwamnan ya tsaya kan bakarsa na kin tattaunawa yan bindigan don sakin daliban.

Abun takaici, an kashe biyar daga cikinsu kuma yan fashin sun lashi takobin ci gaba da kashe su idan har ba a biya su kudin fansar da suka nema ba.

Jim kadan bayan da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace daliban makarantar sakandaren ‘yan mata ta gwamnati, Chibok, jihar Borno, El-Rufai na daya daga cikin manyan muryoyin da suka yi tir da gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce: “Da a ce ɗaya daga cikin waɗannan ’yan matan ’yar Jonathan ce, da labarin ya bambanta. Dalilin da ya sa har yanzu ake tsare da wadannan 'yan matan shi ne saboda ba' ya'yan wani shahararren dan Najeriya ba ne, kuma mun san hakan. Idan ka ce muna sanya siyasa a cikin ta'addanci, je ka kubutar da 'yan matan ta yadda ba zan sami dalilin yin siyasa da shi ba."

Da aka tambaye shi ko yana goyon bayan tattaunawa, sai ya amsa: “Ina goyon bayan duk wani zabi, lokacin da rayuwar ‘yan kasa ke cikin hatsari, bai kamata ku sami wani zabi a kan tebur ba. Ya kamata ku yi tunani kuma ku saurara.”

KU KARANTA KUMA: Tashe-tashen Hankula Sun Karade Ko'ina a Najeriya Yayin Da Wasu 'Yan Bindiga Suka Kashe 'Yan Sanda 9 a Kebbi

A gefe guda, Yan bindiga masu garkuwa da mutanen da suka sace dalibai a jami'ar Greenfield dake jihar Kaduna sun sake bindige biyu cikin kimanin dalibai 22 da suka sace.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta tsinci gawawwakin daliban ne cikin daji.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan jihar, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Litinin.

Source: Legit

Online view pixel