Kano Ta Lalata Jabun Kayayyakin Abinci da Ake Sayarwa Al'umma na Kimanin N1bn

Kano Ta Lalata Jabun Kayayyakin Abinci da Ake Sayarwa Al'umma na Kimanin N1bn

- Gwamnatin jihar Kano ta lalata kayayyakin abincin na jabu na kimanin Naira biliyan daya

- Gwamnatin ta bayyana cewa, ba za ta yi bacci ba har sai ta tabbatar da tsarkake jihar da kayan jabu

- Hakazalika ta yabawa hukumomin da suka taimaka wajen tabbatar da an kame masu laifin

Gwamnatin jihar Kano a ranar Lahadin da ta gabata ta lalata jabun kayayyakin abinci, abubuwan shaye-shaye da magunguna na kimanin Naira biliyan daya, Vanguard ta ruwaito.

Kayayyakin na jabu da aka kiyasta sun kai tan 400 da Hukumar Kula da Masu Amfani da Kayan Masarufi ta Jihar Kano (KSCPC) ta kame su a sassa daban-daban na jihar.

Da yake jawabi lokacin da yake jagorantar shirin lalata kayayyakin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatinsa ta himmatu sosai wajen ganin ta zakulo dubun-dubatar masu aikata laifukan sayar da jabun kayayyaki ga jama'a.

KU KARANTA: 'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kone Ofishin 'Yan Sanda na Mainok ta Jihar Borno

Kano ta lalata jabun kayayyaki da ake sayarwa al'umma na kimanin N1bn
Kano ta lalata jabun kayayyaki da ake sayarwa al'umma na kimanin N1bn Hoto: pressablecdn.com
Asali: UGC

Gwamnan ya bayyana wannan mummunar dabi'ar a matsayin abin da ba za a yarda da shi ba yana mai cewa lokaci ya yi da ya kamata 'yan kasuwar ababen abincin da na shaye-shaye da kuma magunguna su sake tunani.

Ya yaba wa NAFDAC, KAROTA, KSCPC da sanannun jami'an tsaro da suka dauki wannan salo na bin diddigin masu laifin.

A nasa jawabin, Mukaddashin Manajan Darakta na KSCPC, Alhaji Baffa Babba Danagundi ya ce jajircewarsa na yakar matsalar ta samu goyon baya da karfafa gwiwa da suka samu daga Gwamnatin Jihar.

Ya bayyana cewa tallafin sama da Naira Miliyan 50 da suka samu ya matukar karfafa yaki da gurbatattun abinci, abubuwan sha da kuma jabun magunguna.

KU KARANTA: Gwamnan Yobe Ya Gana da Shugaban Hafsoshin Tsaro Kan Batun Boko Haram a Geidam

A wani labarin daban, Ofishin shiyyar Ibadan na Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Zagon Kasa (EFCC) ya kama wani dan kasuwar bitcoin da laifin aikata zamba a yanar gizo, Premium Times ta ruwaito.

Wanda ake zargin, Ayomide Adebowale, an kama shi a ranar Juma’a, tare da wasu mutum hudu daga wasu wurare biyu a yankin Elebu da ke Ibadan ta Jihar Oyo.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana sauran da aka kama da suna Philip Gabriel, Mayowa Jolaoso Segun, Babatunde Segun Adeyinka da Abiodun Tolulope Emmanuel.

Asali: Legit.ng

Online view pixel