Yariman Saudiyya ya Magantu da Mahamat Idriss Deby kan Rasuwar Mahaifinsa

Yariman Saudiyya ya Magantu da Mahamat Idriss Deby kan Rasuwar Mahaifinsa

- Yarima mai jiran gado a kasar Saudiyya ya zanta da sabon shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby

- Ya zanta da Mahamat ta wayar tarho ne inda ya isar da sakonsa ta ta'aziyya kan rasuwar Idriss Deby

- Ya kuma taya kasar da addu'ar zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da dorewarsa a kasar

Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad bin Salman bin Abdulaziz da mataimakin Firaminista da kuma ministan tsaro sun tattauna da shugaban sojin Chadi Mahamat Idriss Deby ta wayar tarho a ranar Lahadi.

Alarabiya News ta ruwaito cewa, Yarima bin Salman ya yi wa Janar Mahamat Deby ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa Idriss Deby wanda ya rasu a ranar Litinin sakamakon samun wasu raunuka a fagen daga.

KU KARANTA: Jerin Kasashen da Suka Mance da Labarin Maleriya Tsawon Shekaru 20

Yariman Saudiyya ya Magantu da Mahamat Idriss Deby kan Rasuwar Mahaifinsa
Yariman Saudiyya ya Magantu da Mahamat Idriss Deby kan Rasuwar Mahaifinsa Hoto: theafricareport.com
Asali: UGC

A bayaninsa, Yariman ya yi wa Chadi fatan dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A nasa bangaren kuma Janar Mahamat ya gode wa Yariman kan karamcin da ya nuna masa.

A makon jiya ne 'yan tawaye a kasar Chadi suka harbe shugaban kasar ta Chadi Idriss Deby yayin wani hari.

Biyo bayan kashe Idriss Deby, an nada dansa Mahamat Idriss Deby a matsayin sabon shugaba na mulkin soja a kasar ta Chadi.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun hari coci, sun kashe likita, sun sace mutane Kaduna

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya ce rasuwar shugaban kasar Chadi Idriss Deby "tabbas zai haifar da babban gurbi a kokarin da ake yi na hada karfi da karfe wajen tunkarar 'yan ta'addan Boko Haram da kuma Daular Musulunci ta Afirka ta Yamma."

Shugaban ya yi wannan bayanin ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin sa Garba Shehu, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Deby ya mutu ne sakamakon raunin da ya samu yayin fada da ‘yan tawaye a arewacin kasar, a cewar sojojin Chadi a safiyar ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel